Bayan Najeriya, ga Cikakken Jerin Kasashen Afirka 7 da Suka Canza Taken Kasa

Bayan Najeriya, ga Cikakken Jerin Kasashen Afirka 7 da Suka Canza Taken Kasa

A ranar Laraba, Shugaba Bola Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar 'taken kasa' ta shekarar 2024 da ta dawo da tsohon taken kasar mai taken "Nigeria, We Hail Thee".

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tun a shekarar 1978 aka daina amfani da taken, inda aka maye gurbin sa da taken, "Arise, O Compatriots," wanda 'yan zamanin nan suka fi sani.

'Yan Najeriya da dama sun nuna adawa da canza taken kasar da Bola Tinubu ya yi yayin da wasu suka nuna a dawo da taken da aka fi iya amfani da shi.

Ba Najeriya ce kadai kasar Afirka da ta sauya taken kasar ba
Jerin kasashen Afirka da suka sauya taken kasar su/ Hoto: @CyrilRamaphosa, @officialABAT
Asali: Twitter

Yadda Tinubu ya canza taken Najeriya

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa majalisar wakilai ta zartar da dokar taken kasa na shekarar 2024 a ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Abubuwan kunya 6 da suka faru da Gwamnatin Tinubu a cikin shekara 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan majalisar dai sun yi zargin cewa taken 'Arise O Compatriot' ya fito ne daga wata doka ta mulkin soja.

Mun ruwaito cewa tun a bikin murnar zagayowar ranar samun 'yancin Najeriya na 2022, Shugaba Bola Tinubu ya ci burin dawo da taken "Nigeria, We Hail Thee".

Wata 'yar Birtaniya, Lilian Jillian Jean William da ta zauna a Najeriya a lokacin ba da 'yanci ne ta rubuta wannan taken, in ji rahoton Premium Times.

Ga jerin kasashen Afrika bakwai (7) da suka sauya taken kasar su.

1. Rwanda - "Rwanda Nziza"

A shekara ta 2001, Rwanda ta soma amfani da taken, 'Rwanda Nziza,' domin karfafa hadin kai da kuma sulhu na kasa bayan kisan kare dangi da aka yi a kasar a shekara ta 1994.

Kasar Rwanda da ke a Afirka ta Gabas ta na daya daga cikin kasashen Afirka da suka sha fama da yakin basasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya burma matsala, lauyoyi za su maka shi a kotu kan wani kuskuren da ya tafka

2. Zimbabwe - "Simudzai Mureza wedu WeZimbabwe"

A shekara ta 1994, Zimbabwe ta bar amfani da taken 'Ishe Komborera Africa' inda ta koma amfani da 'Simudzai Mureza wedu WeZimbabwe' a matsayin taken kasar ta.

Sabon taken ya samo asali daga muradin kasar na kebanta kanta daga taken da sauran kasashen Afrika ke amfani da shi wanda ke nuna tasirin kawance da juna.

3. Afirka ta Kudu - "Nkosi Sikelel' iAfrika"

A cikin shekarar 1997, Afirka ta Kudu ta canza takenta domin nuna sabon zamanin dimokuradiyya bayan mulkin wariyar launin fata.

An hada taken "Nkosi Sikelel' iAfrika" da "Die Stem van Suid-Afrika" domin samar da sabon take a kasar.

4. Dimokuradiyyar Congo - "Arise Congolese"

An amince da taken "Arise Congolese" a matsayin taken Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a cikin shekarar 1960 bayan ta sami 'yancin kai daga Belgium.

A shekara ta 1971, aka canza taken zuwa "La Zaïroise" lokacin da ƙasar ta canza suna zuwa Zaire.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Kamar Najeriya, kasar ta koma amfani da takenta na farko bayan hambarar da gwamnatin Mobutu Sese Seko a shekarar 1997.

5. Ghana - "Lift High the Flag of Ghana"

An fara amfani da taken kasar Ghana na farko "God Bless Our Homeland," a shekarar 1957 lokacin da kasar ke karkashin mulkin mallaka.

Amma a ranar 1 ga watan Yuli, 1960, ƙasar ta zama jamhuriya kuma ta canza taken ta zuwa "Lift High the Flag of Ghana."

6. Namibiya - "Namibia, Land of the Brave"

Kafin samun 'yancin kai daga Afirka ta Kudu, taken kasar Namibiya a hukumance shi ne "Die Stem van Suid-Afrika," wanda kuma shi ne taken kasar Afirka ta Kudu.

Amma bayan da Namibia ta samu 'yancin kai, ta koma amfani da "Namibia, Land of the Brave" a matsayin taken ta domin nuna ikon mallakar kasar da kuma alfaharin ta.

7. Libiya - "Libya, Libya, Libya"

A yunkurinsa na hada kan kasashen Larabawa na Afirka da Asiya, Mu'ammar Gaddafi ya maye gurbin taken kasar "Libya Libya Libya" da "Allahu Akbar" a shekarar 1969.

Kara karanta wannan

Shekara 1 a ofis: Jerin ministoci 10 da suka fi kowa kokari a gwamnatin Tinubu

Sai dai a watan Oktoban 2011, bayan yakin basasar Libya da kuma mutuwar Gaddafi, Majalisar wucin gadin kasar ta sake dawo da "Libya, Libya, Libya" a matsayin sabon taken kasar.

Taken kasa: Abin da 'yan Najeriya ke cewa

A zantawar mu da wasu 'yan Najeriya, sun bayyana ra'ayin su kan sauya taken Najeriya da aka yi.

Muhammad Al'ameen daga jihar Kaduna, ya bayyana cewa sauya taken ba shi ne 'yan kasa ke bukata a yanzu ba, duk da yana da ma'ana.

Al'ameen ya ce kamata ya yi ace majalisu da gwamnatin tarayya sun damu da matsin tattalin arziki da kuma samar da hanyoyin saka abinci a kwanukan 'yan kasar.

Ibrahim Maiduna ya tambaya:

"Mu da muka gama jami'a, me amfani sauya wannan taken a wajen mu tunda ba tara mu za a yi mu yi bita ba?"

Maiduna ya ce tsohon taken kasar ya fi dadi wajen karantawa amma kuma wanda aka sauya ya fi fitar da ma'ana.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya cika burin da ya dauka a 2022, ya dawo da tsohon taken Najeriya

Tinubu ya amince da dokar taken kasa

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokar mayar da Najeriya amfani da tsohon taken kasar da ubangidanta na mulkin mallaka ya yi.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da rattaba hannun Tinubu kan dokar a zaman hadin gwiwa da suka yi a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel