Maganin Duhu: Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Aron $500m Daga Bankin Duniya
- Gwamnatin tarayya ta samu damar karbo rancen $500m daga bankin duniya domin farfado da bangaren rarraba hasken wutar lantarki ga 'yan kasa yayin da ta yi karanci
- A sanarwar da shugabar sashen hulda labaran hukumar kula da kadarorin gwamnati ta fitar, Amina Tukur Othman ta ce za a yi amfani da kudin wajen tallafawa kamfanonin DisCos
- Daga abubuwan da ake sa ran za a yi da kudin akwai ware $155m da za a sayi mitoci da su domin rarrabawa 'yan kasa wanda zai taimaka wajen wadata al'umma da wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hukumar da ke lura da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin magance matsalar hasken wuta a kasar.
BPE ta sanar da cewa gwamnati ta yi nasarar karbo rancen $500m domin taimakawa kamfanonin rarraba hasken wuta (DisCos) domin magance matsalolin wuta
Bankin Duniya zai ba Najeriya $500m
Nigerian Tribune ta tattaro cewa rancen da bankin ya amince da shi a shekarar 2021 zai taimakawa shirin gwamnati na farfado da rarraba hasken wuta a Najeriya (DISREP).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta bayyana cewa za a yi amfani da kudin wajen cicciba kamfanonin DisCos wajen samawa 'yan Najeriya wuta.
Ta ya DisCos za su amfana da bashin?
A sanarwar da shugabar sashen hulda labaran hukumar, Amina Tukur Othman ta lissafa yadda DisCos za su ci gajiyar shirin har ya fado kan 'yan kasa.
Ta ce wasu daga abubuwan da za ayi da makudan kudin su ne sayen mitoci, da sauran kayan adana bayanai domin ta haka za ta samu sukuni. Haka kuma za a yi amfani da $345m wajen dabbaka wasu ayyukan hukumar, sai $155m da su ne za a sayi mitocin wuta.
Amina Tukur Othman ta kara da cewa hukumar ta nemi taimakon babban bankin kasa CBN, kamar yadda The Nation ta wallafa.
Nijar, wasu kasashe sun hana kudin wuta
A baya mun samu rahoton yadda wasu kasashe da ke makwabtaka da Najeriya su ka hana kudin wutar da aka ba su a shekarar 2023.
Hukumar kula da hasken wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana haka, inda ta lissafa kasashen da suka ci bashi da Togo, Cameroon da jamhuriyyar Nijar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng