EFCC Ta Dauko Binciken Kwankwaso Ana Cikin Rikicin Masarautar Kano
- Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta fara bincike kan zargin da ake yiwa Rabiu Musa Kwankwaso kan karkatar da N2.5bn
- Kuɗaɗen da ake zargin Kwankwaso da tawagarsa sun karkatar na yaƙin neman zaɓen jam'iyyar NNPP ne a lokacin zaɓen shekarar 2023
- EFCC ta gayyaci wanda ya shigar da ƙorafi kan Kwankwaso wanda hakan ke nuna nan ba da jimawa ba za a gayyaci tsohon gwamnan domin ya kare kansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta fara bincike kan zargin karkatar da kuɗin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar NNPP ƙarƙashin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.
Zargin ya kuma haɗa da rashin biyan wakilan jam'iyyar kuɗinsu saboda aikin da suka yiwa jam'iyyar a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni a shekarar 2023.
An fara binciken Kwankwaso a EFCC
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hukumar EFCC ta gayyaci sakataren jam'iyyar na ƙasa, Oginni Olaposi Sunday, domin tabbatar da zarge-zargen da ake yi a kan Kwankwaso da sakatariyarsa ta musamman Folashade Aliu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tabbatar da lamarin yayin wata hira ta wayar tarho da jaridar, Olaposi Oginni ya bayyana cewa ya halarci hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja ranar Laraba ta makon da ya gabata.
Ya ce ya je hedkwatar hukumar ne domin ya yi ƙarin bayani kan ƙorafin da ya shigar a madadin jam'iyyar kan cewa Kwankwaso da tawagarsa sun karkatar da N2.5bn na NNPP.
Shugaban NNPP ya tabbatar da batun EFCC
"Eh tabbas EFCC ta gayyace ni. Na amsa gayyatar kuma na gamsu da sanin makamar aikin jami'an EFCC. Na amsa tambayoyi kan ƙorafin da na shigar a madadin NNPP ba tare da wata tsangwama ko muzgunawa ba.
"Suna so su samu tabbaci cewa zarge-zargen da gaske ne sannan ba domin wata mummunar manufa aka yi su ba."
- Oginni Olaposi Sunday
Yaushe EFCC za ta gayyaci Kwankwaso?
Duba da tabbacin gayyatar da EFCC ta yiwa sakataren jam'iyyar NNPP na ƙasa, a bayyane yake cewa an fara bincike kan ƙarar da aka shigar a kan Rabiu Musa Kwankwaso.
Hakan na nufin nan ba da jimawa ba hukumar za ta gayyace shi domin ya kare kansa daga zarge-zargen.
Kwankwaso zai binciki dawo da Sanusi II
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce bai sa baki a mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karaga ba.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce nan kusa zai koma Kano kuma zai gano yadda aka yi aka mayar da Khalifan Tijjaniya kan mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng