Barauniya Ta Raba Mai Jego da Jaririn Wata 1, Ta Fada Hannun Jami'an Tsaro

Barauniya Ta Raba Mai Jego da Jaririn Wata 1, Ta Fada Hannun Jami'an Tsaro

  • Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bayyana cafke wata mata mai suna Blessing bisa zargin shiga har cikin gida tare da sace wani jariri dan wata daya
  • Mahaifiyar jaririn ce ta garzaya ofishin ‘yan sandan Elere inda ta ce tana barci da sanyin safiyar Asabar lokacin da matar ta lallaba ta dauke mata jariri
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya ce tuni aka kama matar a Agbotikuyo da ke Agege kuma ta shaidawa mutane cewa 'danta ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos- Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta samu nasarar damke wata mata mai shekaru 21 da jaririn da ta sato a gaban mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Masarauta: 'Yan sanda sun goyi bayan Gwamnan Kano, an gargadi masu shirin rigima

Mahaifiyar jaririn da aka sakaye sunanta ce ta kai rahoto ga ‘yan sandan Elere a ranar Litinin tana korafin yadda wata mata Blessing ta sace mata yaro.

Lagos State Police Command
Yan sanda sun kama barauniyar jariri a Lagos Hoto: Lagos State Police Command
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da cafke matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Blessing ta sace jariri a Lagos

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, SP Benjamin Hundeyin ya shaidawa manema labarai cewa wanda ake zargi ta lallaba ta sace jaririn ne har cikin gida.

Ya ce jaririn 'dan wata daya na kusa da mahaifiyarsa da ke barci a lokacin da aka yi satar da misalin karfe 7.00 na safe, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Kakakin ya kara da cewa matar da garzaya coci tana neman a taya ta murna ta samu haihuwa. kuma an cafke ta a unguwar Agbotikuyo da ke Agege ta jihar.

Kara karanta wannan

An dauki mataki kan 'dan sandan da aka nadi bidiyonsa yana karbar 'na goro' a Imo

Alhajin Lagos ya rasu a Saudiyya

Mun kawo muku labarin cewa wani maniyyacin aikin hajjin bana daga jihar Lagos, Idris Olosogbo ya riga mu gidan gaskiya jim kadan bayan sauka a kasa mai tsarki.

Babban sakataren hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Saheed Onipede ya tabbatar da lamarin tare da bayar da tabbatar da cewa tuni aka yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel