Tumatur Ya Yi Tsada a Najeriya, Manoma Sun Fadi Abin da Ya Sa Jar Miya Ta Gagara
- A yayin da mafi yawan kayan masarufi suke kara tsada a Najeriya, kayan miya sun shiga sahun abubuwan da suka kara kudi
- A gefe guda, farashin danyen tumatur ya yi tashin gauron zabi tare da wahalar samuwa a mafi yawan kasuwannin Najeriya
- Legit ta tattauna da mai noman tumatur a garin Kwadon da ke jihar Gombe domin jin yadda nomar rani ta gudana a yankin su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fitar na cigaba da kawo tsadar kayan masarufi a kasuwannin Najeriya.
A kwanan nan an fara samun tsadar kayan miya a bangarori da dama na Arewaci da kudancin Najeriya.
Wasu manoma a jihar Bauchi sun bayyanawa jaridar Daily Trust dalilan da suka jawo karanci da tsadar tumatur a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin tsadar tumatur a Najeriya
Masu nomar rani a jihar Bauchi sun bayyana cewa karin kudin mai da kudin wuta suna cikin abubuwan da suka hana mutane da dama noman rani a Najeriya.
Sun ce rashin nomar yadda ya kamata ya haifar da ƙarancin tumatur a kasuwanni wanda ya jawo tsadarsa sosai.
Karin haske daga shugaban manoma
Shugaban masu noman rani a jihar Bauchi, Alhaji Sani Abubakar ya ce dole farashin ya cigaba da tashi saboda matsaloli da dama.
Ya ce matuƙar ba a samo mafita ga abubuwan da suka jawo tashin farashin ba to dole zai cigaba da haurawa a kowace rana.
Yadda farashin kayan miya ya tashi
Shugaban manoman ya bayyana cewa tashin farashin ya shafi dukkan kayan miya da ake nomawa a rani.
A cewarsa, a bara sun sayar da buhun tattasai a N2,500 amma a yau saboda matsalolin tattalin arziki suna sayar da shi a N60,000 zuwa N80,000.
Legit ta tattauna da mai nomar rani
Legit ta tattauna da wani manomi a garin Kwadon, Usman Muhammad domin jin yadda nomar rani ta gudana a yankin su.
Usman ya tabbatarwa Legit cewa tsadar man fetur ta shafi nomar rani a Kwadon ta inda manoma da yawa sun ajiye noma a wannar shekarar.
Dalilin karin kudin wutar lantarki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya, ta ce ta janye tallafin wutar lantarki ne domin wadatar da wutar a Nijeriya nan da shekara uku masu zuwa.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce dole 'yan Najeriya za su biyan kudin wuta da tsada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng