Majalisa Ta Ɗauki Mataki Kan Korar Daraktoci da Manyan Ma'aikata a Bankin CBN

Majalisa Ta Ɗauki Mataki Kan Korar Daraktoci da Manyan Ma'aikata a Bankin CBN

  • Batun korar daraktoci da manyan ma'aikata a babban bankin Najeriya ya ja hankalin majalisar wakilan tarayya a ranar Laraba
  • Majalisar za ta binciki yadda aka yi aka rubutuwa ma'aikata akalla 600 takardar kora a CBN bayan ta amince da wani kudiri da aka gabatar
  • Ta bai wa kwamitoci biyu aikin gudanar da wannan bincike kuma su dawo da rahoton abin da suka gano cikin makonni huɗu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ɗaura niyyar gudanar da bincike kan yadda aka yi aka raba ƴan Najeriya akalla 600 da aikinsu a babban bankin Najeriya (CBN).

Majalisar ta cimma wannan matsaya bayan amincewa da kudirin hanzari wanda Honorabul Jonathan Gbefwi (SDP, Nasarawa) ya gabatar a zauren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP ya dau zafi kan yadda CBN ya kori ma’aikata 317, majalisa za ta yi bincike

Majalisar dokoki ta ƙasa.
Majalisar wakilai za ta duba yadda ake sallamar ma'aikata a CBN Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisa ta kawo zancen korar ma'aikatan CBN

Da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar ya ce ma'aikata sama da 600 sun rasa aikinsu a CBN a wani ɓangare na kokarin sake fasalin ayyukan babban bankin, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin da CBN ya aikata ya haifar da damuwa da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu ruwa da tsaki kama daga ma’aikatan da aka kora, kungiyoyin kwadago da sauran jama’a.

Dan majalisar ya koka da cewa wadanda bankin CBN ya kora kwararru ne kuma ƙasahen Turai da Amurka ka iya zuwa su ɗauke su, su bar Najeriya tana ci baya.

CBN: 'Yan majalisa sun soki korar ma'aikata

Gbefwi ya nuna damuwarsa cewa irin waɗannan matakai na kora ba tare da sauraren ma'aikatan ko bincike ba ka iya jawo ma ƙasar nan koma bayan da ba a tunani.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cin kwakwa, Majalisa ta sauya taken Najeriya, ta fadi amfaninsa

Idan ba ku manta ba a rahoton da muka kawo maku, waɗanda CBN ya kora sun haɗa da daraktoci, mataimakansu, manyan manajoji da ma'aikata.

Da yake jawabi kan aikin daraktoci, Honorabil Gbefwi ya ce:

“Wa’adin darakta bisa ka’idar aikin gwamnati shi ne wa’adi biyu na shekara hudu watau shekaru takwas kenan ko kuma shekarun aiki 60, duk wanda ya fara cika shikenan.
"Wannan ya sa suka zama kamar manyan sakatarori. Abin tambayar shi ne za a iya maye gurbin kwarewar waɗanda aka kora cikin sauƙi?"

Wani mataki majalisar tarayya ta fara dauka?

Da take amincewa da kudirin, majalisar ta umurci kwamitocin kula da harkokin banki da kuma tsarin tarayya da su duba yadda ake garambawul a CBN.

Kuma ta umarci su binciki dalilin da ya sa ake rage yawan ma'aikata a babban bankin kana su dawo da rahoto cikin makonni huɗu, The Cable ta ruwaito.

Tinubu ya faɗi waɗanda suka taimake shi

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

A wani rahoton kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wadanda suka masa sharar fage har ya samu damar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a Najeriya.

Bola Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake kaddamar da sabon taken Najeriya a majalisar dattawan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262