'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Ɗalibai Mata a Jami'ar Tarayya a Arewa

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Ɗalibai Mata a Jami'ar Tarayya a Arewa

  • Wasu mahara sun tare daliban jami'a mata, sun yi awon gaba da su a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ranar Asabar
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa an sace ɗalibai mata biyu na jami'ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM)
  • Ta ce tuni jami'an ƴan sanda suka fara bincike domin kubutar da ɗaliban bayan samun rahoto daga hukumar jami'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Laraba ta tabbatar da sace wasu dalibai mata biyu na jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM).

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an yi garkuwa da daliban ne a daren ranar Asabar a kan hanyar zuwa makarantar da a baya ake kiranta da sunan jami'ar noma ta tarayya (FUAM).

Kara karanta wannan

Katsina: An kama mutum 2 da hannu a sace mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
An yi garkuwa da ɗaliban jami'a mata a jihar Benuwai Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

'Yan sanda sun tabbatar da sace dalibai

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sanda reshen jihar, SP Catherine Anene ce ta tabbatar da sace ɗaliban ga manema labarai a Makurɗi, babban birnin Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kakakin rundunar ƴan sandar ba ta ambaci sunayen ɗaliban da aka yi garkuwa da su ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yadda aka sace ɗaliban JOSTUM

Amma Anene ta yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 11 na dare a kan titin North Bank/UniAgric dake Makurdi.

Ta kuma tabbatar da cewa harin da aka kai har aka ɗauke ɗaliban ya faru ne a wajen makaranta amma ba a cikin harabar jami'a ba.

Ta ce masu garkuwar da mutanen sun tare hanya, kana suka ɗauki ɗaliban suka tafi da su kafin jami’an tsaro su isa wurin.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Anene ta ce tuni iyalan ɗaliban da aka sace da hukumar makarantar suka sanar da ‘yan sanda kuma an fara gudanar da bincike kan lamarin, cewar Daily Post.

Mataimakiyar shugaba mai kula da sashin yada labarai da hulda da jama'a, Misis Lucy Iwodi, ta shaida wa manema labarai lokacin da aka tuntube ta cewa ba ta samu izinin yin magana kan lamarin ba.

Ƴan bindiga sun farmaki kasuwa a Kaduna

A wani labarin ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru da tsakar rana a ranar Laraba, 29 gs watan Mayun 2024.

Maharan sun kai harin ne a kasuwar Kwanar Maro a gundumar Maro a ƙaramar hukumar yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel