'Yan Ta'adda Sun Kai Farmaki Cikin Kasuwa a Kaduna, An Rasa Rayukan Bayin Allah

'Yan Ta'adda Sun Kai Farmaki Cikin Kasuwa a Kaduna, An Rasa Rayukan Bayin Allah

  • Ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru da tsakar rana a ranar Laraba, 29 gs watan Mayun 2024
  • Ƴan ta'addan sun kai harin ne a kasuwar Kwanar Maro a gundumar Maro a ƙaramar hukumar yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci
  • Mutum 12 ne suka rasa rayukansu yayin da aka raunata wasu mutum 20 a harin da ƴan ta'addan suka kai cikin kasuwar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan ta’adda sun ai hari tare da kashe mutum 12 a kasuwar mako-mako ta Kwanar Maro, a gundumar Maro, ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Ƴan ta'addan sun farmaki kasuwar ne yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki masunta a Borno, an rasa rayukan mutum 15

'Yan ta'adda sun hallaka mutum 12 a Kaduna
'Yan ta'adda sun kashe mutum 12 a wani hari a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kajuru, Cafra Caino, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan ta'adda suka kai harin

Cafra Caino ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun farmaki kasuwar ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana sannan suka buɗe wuta kan mutane.

A cewarsa, an gano gawarwakin mutum 12 yayin da wasu mutum 20 da suka samu raunuka daban-daban kuma an kai su wani asibiti da ke kusa domin yi musu magani.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da aka kai hari a kasuwar mako-mako a yayin da ƴan kasuwa da masu yin sayayya ke gudanar da harkokin kasuwanci.

Mutane sun shiga fargabar 'yan ta'adda

Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin rudani yayin da wasu suka tsere domin tsira da rayukansu zuwa ƙauyukan da ke makwabtaka da su.

Kara karanta wannan

Wani shugaban ƴan bindiga ya gamu da ajalinsa yayin da suka kai hari a Katsina

"Jami'an tsaron da aka kai yankin sun bar wurin. Muna kira ga gwamnati da ta tura jami’an tsaro domin su taimaka wajen dawo da zaman lafiya."

- Cafra Caino

'Yan sanda sun san da harin 'yan ta'addan?

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan kan halin da ake ciki.

Sai dai jami'in bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba, sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a wasu hare-hare a jihohin Borno da Katsina.

Sojojin saman sun hallaka ƴan ta'adda 30 bayan sun yi musu luguden wuta a maɓoyarsu da ke cikin daji a hare-haren.

Kara karanta wannan

An hallaka mutum 2 yayin gwabzawar 'yan sanda da masu garkuwa da mutane a Kogi

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel