Sanusi II Vs Aminu: 'Yan Majalisan Kano 12 Sun Yi Mubaya'a ga Sarki Na 15
- Mambobi 12 na majalisar dokokin jihar Kano sun yi mubaya'a ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero a ƙaramar fadar Nasarawa
- Ƴan majalisar na jam'iyyar APC sun ziyarci basaraken a fadar da yake zaune a ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024
- Wannan mataki da suka ɗauka na zuwa ne a lokacin da rikicin sarautar Kano ya buɗe sabon babi bayan kotuna sun bayar da umarni daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Yayin da rigimar sarauta ke ƙara ƙamari a jihar Kano, ƴan majalisa 12 na APC a majalisar dokoki sun yi mubaya'a ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Bisa jagorancin shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari, mambobin majalisar na APC sun kai ziyara ga Aminu Ado a ƙaramar fadar Nassarawa.
'Yan APC sun ziyarci Sarki Aminu Ado
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ƴan majalisar sun ziyarci basaraken ne jim kaɗan bayan fitowa daga zaman majalisar dokokin Kano ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba rikicin sarauta ya ɓarke ne tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero dai sun ki biyayya ga umarnin kotu daban-daban na neman su fice daga fadar sarkin da suke zaune.
Yayin da ‘yan majalisar APC a majalisar dokokin jihar suka kai ziyara ga Aminu Ado Bayero ba, kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari sun ziyarci Sanusi ranar Talata.
Ƴan kasuwa sun je wajen Sanusi II
Tawagar ƴan kasuwar karƙashin kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya, sun ziyarci Sarki Sanusi II a fadar Kofar Kudu.
Ƴan kasuwar sun yi mubaya'a tare da tabbatar da goyon bayansu ga Sarki Muhammadu Sanusi II, rahoton Solabase.
Tun ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sarki Sanusi ke karbar baki masu zuwa domin yin mubaya’a, ciki har da hakimai da masu rike da mukaman sarauta 40.
Bincike ya nuna cewa kungiyoyin ’yan banga da mafarauta (Yan Tauri) na ci gaba sintiri da sa ido a fadar.
Haka nan an ga jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS 5 a kofar shiga daya daga cikin ofisoshin sarkin da ke Gidan Rumfa.
Dattaawan kudancin Kano sun ɗauki matsaya
A wani rahoton kuma, masu ruwa da tsaki a yankin masarautun Gaya, Karaye da Rano sun yi fatali da rushe masarautu biyar da Abba Yusuf ya yi a Kano.
Dattawan sun buƙaci gwamnatin jihar Kano da majalisar dokoki su bi umarnin babbar kotun tarayya wadda ta hana rushe masarautun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng