Rikicin Masarauta: Alkalin Alkalai Ya Dauki Mataki Kan Alkalan Kotunan Kano

Rikicin Masarauta: Alkalin Alkalai Ya Dauki Mataki Kan Alkalan Kotunan Kano

  • Alƙalin alƙalan Najeriya, mai shari'a Olukayode Ariwoola ya gayyaci alƙalan manyan kotunan Kano kan rikicin masarauta
  • Mai shari'a Olukayode ya gayyaci alƙalan babbar kotun tarayya da kuma shugaban alkalan kotun jihar Kano a ranar Laraba
  • Gayyatar da aka yiwa alƙalan na da nasaba da umarnin da suka bayar waɗanda suka ci karo da juna kan taƙaddamar sarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano- Babban alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci babban alƙalin babbar kotun tarayya da kuma babban alƙalin kotun jihar Kano.

Olukayode Ariwoola ya gayyaci alƙalan ne kan wasu hukunce-hukuncen wucin gadi da suka yi dangane da masarautar Kano, lamarin da ya haifar da rashin tabbas a jihar.

Kara karanta wannan

Kungiyar sarakuna ta ba Sanusi II shawara kan rikicin masarautar Kano

CJN ya gayyaci alkalan manyan kotunan Kano
CJN ya gayyaci alkalan manyan kotunan Kano kan rikicin masarautar Kano Hoto: @Super_Joyce1, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: UGC

Tashar Channels tv ta kawo rahoto kan gayyatar da mai shari'a Olukayode Ariwoola ya yiwa alƙalan a ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masarautar Kano: Alƙalai sun kawo ruɗani

Babbar kotun tarayya da ke Kano ƙarƙashin mai Shari’a S. A. Amobeda, ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar Kofar Kudu, inda ta ƙara ƙarfafa ikon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

A ɗaya hannun kuma, babbar kotun jihar Kano a ƙarƙashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kare Muhammadu Sanusi II da sauran manyan mutane daga cin zarafi daga jami'an tsaro.

Sarkin Kano ya samu kariya a kotu

Wannan umarnin ya hana duk wani katsalandan ga ikon Sarkin da kuma ƙwace manyan alamomin ikonsa, kamar tagwayen masu, hular sarauta ta Dabo, da takalman gashin jimina.

Kara karanta wannan

Rushe masarautu: Gwamnatin Kano ta sanya sabuwar doka kan masu zanga zanga

Waɗannan umarnin da suka ci karo da juna sun haifar da ruɗani mai yawa dangane da kare martabar Sarakunan na Kano.

A ranar 13 ga watan Yuni ne za a ci gaba da sauraren ƙarar babbar kotun jihar, yayin da babbar kotun tarayya ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Yuni.

Sarakuna sun ba Sanusi II shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar sarakuna ta shawarci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da ya fice daga fadar Sarkin Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci Sanusi II da ya mutunta umarnin kotu wanda ta ce a fitar da shi daga fadar Sarkin na Kano saboda a samu kwanciyar hankali a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel