Rushe Masarautu: Kungiya Ta Mika Kokon Bara Ga Majalisar Dokokin Kano

Rushe Masarautu: Kungiya Ta Mika Kokon Bara Ga Majalisar Dokokin Kano

  • Ƙungiyar Inuwar Masarautar Bichi ta buƙaci majalisar dokokin jihar Kano ta sauya dokar da ta rushe sababbin masarautun jihar Kano
  • Sakataren ƙungiyar ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta yi duba da abin da jama'a suke so kafin ta amince da dokar ba
  • Ya yi.bayanin cewa rushe masarautun ya jawo mutum 3000 sun rasa ayyukansu, kuma ya yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Masarautar Bichi, ƙarƙashin ƙungiyar Inuwar Masarautar Bichi ta Kano a ta buƙaci majalisar dojojin jihar ta soke dokar da ta rushe sababbin masarautun Kano.

Inuwar Masarautar Bichi ta buƙaci majalisar da ta mayar da sabuwar dokar zuwa ga dokar da ta kafa masarautu biyar da suka samar da sarakuna biyar masu daraja ta ɗaya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

An bukaci majalisar Kano ta sauya dokar rushe masarautu
An bukaci majalisar dokokin Kano ta sauya dokar rushe masarautu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wane gargaɗi aka yiwa gwamnatin Kano?

Jaridar The Nation ta ce sakataren Inuwar Masarautar Bichi, Injiya Bello Gambo, wanda ya yi magana a madadin ƙungiyar, shi ne ya bayyana hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Gambo ya gargaɗi gwamnatin jihar kan aiwatar da sabuwar dokar sannan ta ba da dama masarautun su ci gaba da wanzuwa domin amfanin jihar.

Ƙungiyar ta shaidawa manema labarai a Kano cewa sabuwar dokar da kuma soke masarautun biyar ba abu ne wanda za a amince da shi ba.

Bello Gambo ya ce rusa masarautun zai sa al’ummar yankin sama da 3000 su rasa ayyukansu, wanda hakan zai iya haifar da matsalar rashin tsaro, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

An soki gwamnatin Kano kan rushe masarautu

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba tayi nazari ba sannan ba tayi la'akari da abin da jama'a suke so ba kafin ta rushe masarautun.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta roki sarkin Kano 15 Aminu Ado Bayero ya rungumi kaddara

"Gwamnatin jiha ba ta yi nazari ba wajen rushe masarautun sannan ba ta yi duba da yadda masarautun ke samar da ci gaba a fannin kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa na karkara da dai sauransu."
"Ba za mu amince da shirin gwamnati na naɗa mana sarakuna masu daraja ta biyu ko Dagatai ba. Abin da kawai muke so shi ne Sarkinmu."
"A bar Sarkinmu ya ci gaba da mulki. Ba zamu amince da wani abu ba bayan wannan."

- Injiniya Bello Gambo

Umarnin kotu kan Sarki Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kamo, ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II daga cikin fadar Sarkin Kano.

Alƙalin kotun wanda ya bayar da umarnin ya ce ya yi hakan ne domin tabbatar da adalci da wanzar da zaman lafiya a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel