Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Jawabin Tinubu ga 'Yan Majalisun Tarayya

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Jawabin Tinubu ga 'Yan Majalisun Tarayya

  • Fadar shugaban ƙasa ta fito ta musanta rahotannin da ke yawo masu cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga ƴan majalisun tarayya
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale a cikin wata sanarwa ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya tsagwaronta
  • Rahotanni dai sun ce shugaban ƙasan zai yi jawabi ne a tare ga taron ƴan majalisun tarayyar a ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga majalisun tarayya guda biyu a ranar Laraba.

Rahotannin dai sun ce shugaban ƙasan zai yi jawabi ne ga majalisun biyu a tare domin murnar cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Mun shirya tsaf," 'Yan sanda sun ƙara ɗaukar mataki kan rigimar sarautar Kano

Fadar shugaban kasa ta yi magana kan batun jawabin Tinubu ga majalisun tarayya
Fadar Shugaban kasa ta ce Tinubu ba zai yi jawabi ba ga taron 'yan majalisun tarayya a ranar 29 ga watan Mayu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya ce babu jawabi a majalisa

Mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale ne ya musanta rahotannin jawabin shugaban ƙasan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Ajuri Ngelale ya bayyana cewa batun jawabin shugaban ƙasan ga majalisun guda biyu a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ƙarya ne.

"Duba da bayanan da ake yi dangane da shugaban ƙasa zai yi jawabi ga zaman majalisun tarayya na tare a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun 2024, yana da muhimmanci a bayyana cewa wannan bayanin ƙarya ne.
Kuma ba a amince da hakan ba. Ofishin shugaban ƙasa ba shi da hannu a wajen shirya taron"

- Ajuri Ngelale

Tinubu za yi jawabin cika shekara a ofis?

Idan ba a manta ba dai, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar Talata ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi jawabi ga ƴan ƙasa ba a ranar Laraba domin murnar cikarsa shekara ɗaya kan mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

A maimakon hakan, Onanuga ya ce Tinubu zai yi jawabi ga taron majalisun tarayyar domin tunawa da cika shekara 25 da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sai dai kuma wani mai magana da yawun shugaban ƙasan ya ƙaryata hakan.

Obasanjo ya caccaki gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu manufofin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar a matsayin waɗanda akwai kura-kurai a cikinsu.

Obasanjo ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da mayar da canjin kuɗi kan farashin bai ɗaya manufofi ne da suka dace amma an aiwatar da su bisa kuskure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng