Ana Tsaka da Ruɗanin Hukuncin Kotuna 2, Jigon NNPP Ya Yi Magana Kan Naɗin Sarkin Kano

Ana Tsaka da Ruɗanin Hukuncin Kotuna 2, Jigon NNPP Ya Yi Magana Kan Naɗin Sarkin Kano

  • Yayin da rigimar sarauta ke kara ƙamari a Kano, jigon NNPP ya yaba da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar Sarkin Kano
  • Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP a jihar Ogun, Ambasada Olufemi Ajadi ya ce Kano za ta ƙara bunƙasa a karkashin Sarki Sanusi II
  • Ajadi ya yi kira ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero da magoya bayansa su haƙura su bar zaman lafiya ya zauna kamar yadda aka saba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani jigo a New Nigeria People's Party (NNPP), Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya yaba da dawowar Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Idan ba ku manta ba tsohuwar gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta sauke Sanusi II bayan majalisar dokoki, ta kirkiro masarautu biyar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Muhammadu Sanusi II
Jigon NNPP ya yaba da mayar da Sanusi II kan karagar sarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Twitter

Muhammadu Sanusi II ya dawo sarautar Kano

Kamar yadda Tribune Nigeria ta tattaro, Sanusi II ya koma kan karagar sarauta ranar Jumu'a da ta gabata bayan majalisar dokokin Kano ta rushe masarautun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar da majalisar dokokin ta sabunta a wani taro da ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Kano ranar Alhamis, cewar Premium Times.

Ajadi ya yaba da dawowar Sanusi II

Da yake mayar da martani kan lamarin, Ajadi, ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar NNPP a zaɓen 2023, ya yaba da mayar da Sanusi II kan kujerar sarautar Kano.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Ajadi ya yi kira ga sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da magoya bayansa su bari a ci gaba da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Cakwakiyar da aka sani game da Alkalin da ya dakatar da nada sabon Sarkin Kano

A cewar tsohon ɗan takarar gwamnan, ya zama wajibi mutane su riƙa mutunta doka da oda a kowane lokaci.

Ambasada Ajadi ya ce:

"Na yi matuƙar farin ciki da dawowar Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta, ina da yaƙinin duba da ilimi da gogewarsa, birnin Kano zai ƙara samun ci gaba a ƙarƙashinsa.
“Ina jinjina masa bisa mutunta doka ta hanyar lumana da biyayya ga dokar da tsohuwar majalisar dokokin jihar ta kafa wadda ta kai ga tsige shi.
"Ina masa fatan Allah ya kara masa lafiya tare da fatan bayar da gudunmawar da za ta kawo ci gaban jihar Kano da kasa baki daya inda ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya."

Wani ɗan Kwankwasiya kuma jigo a NNPP, Sa'idu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa kusan kowa ne bakano ya ji daɗin dawowar Sanusi II.

Ya ce duk wanda ka gani baya jin ɗaɗin wannan abu to ɗan APC aƙida ne, amma kusan kaso 80 na mutanen Kano murna suke yi da dawowar sarki.

Kara karanta wannan

Rikicin sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf ya yi shaguɓe ga Aminu Ado Bayero

Ya ce:

"Sarki Sanusi yana da ilimi kuma sananne ne a ƙasar ɓan da ma duniya baki ɗaya, Allah kaɗai ya san mutanen da ke amfana idan yana kan sarauta.
"Ni na san waɗanda ke cin abinci a gidan sarki lokacinsa, amma tun da ya tafi shikenan, na san waɗanda ya samar wa aiki da sauran irin waɗannan abubuwan.
"Don haka muna farin ciki da mayar da shi, fatan mu Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a kansa."

Kotu ta umarci a fitar da Sanusi II

A wani rahoton kuma babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ba umarnin fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano da ke Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma hana waɗanda ake ƙara daga gayyata, kamu ko muzgunawa Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero wanda gwamnati ta ce ta sauke.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262