Kisan Mutane 4,500 da Abubuwan da Suka Faru na Matsalar Tsaro a Mulkin Tinubu
Abuja - A jawabinsa na farko bayan ya karɓi mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Ba wannan ne karon farko da Bola Tinubu ya yi alkawarin inganta tsaro ba. Ya ɗauki alƙawarin kawar da matsalar tsaro a lokuta da dama a kakar zaɓen 2023.
Tsaro a shekarar farko a mulkin Tinubu
Sai dai kuma shekara guda da hawansa mulki, har yanzu kusan dukkanin sassan kasar nan suna fama da matsalar rashin tsaro kala daban-daban, Premium Times ta ruwaito.
Duk da shekara ɗaya ba ta isa a yiwa gwamnati alƙalancin samun nasara ko akasin haka ba, amma dai babu wani ci gaba a ɓangaren tsaro tun da Buhari ga sauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar ta ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, wanda ya kai ga asarar rayuka sama da 4,556 da kuma garkuwa da mutane 7,086 tsakanin 29 ga Mayu 2023 zuwa 22 ga Mayu 2024.
Watanni biyu bayan ya kama aiki, Shugaba Tinubu ya nuna gamsuwa da kamun ludayin sababbin hafoshin tsaron da ya naɗa wata ɗaya tal da kama aikinsu.
Arewa na fama da matsalar 'yan bindiga
Rahoton ACLED da jaridar ta tattaro ya nuna cewa shiyyoyi shidan kasar da Abuja, sun fuskanci tashe-tashen hankula da dama a shekara ɗayan Tinubu.
Matsalar ƴan biindiga a Arewa maso Yamma ita ce a kan gaba, inda aka rasa rayukan mutane 1,475 tare da yin garkuwa da mutane 4,343.
Jihohi uku da suka kunshi Kaduna, Katsina da Zamfara su ne matsalar ta fi yiwa illa, suna da 551 daga cikin hare-hare 718 da aka samu a yankin.
A Arewa ta tsakiya, an samu hare-hare 552 na ‘yan fashi, rikicin manoma da makiyaya da kuma kungiyoyin asiri, wanda ya jawo asarar rayuka 1,444, ciki har da sojoji da jami’an tsaro.
Har ila yau, tayar da ƙayar baya, ‘yan bindiga da sauran nau’ukan miyagun laifuka a Arewa maso Gabas sun yi sanadin mutuwar mutane 819 tare da yin garkuwa da mutane 688.
Ƙungiyoyin asiri da ƴan bindiga a Kudu
A jimillar tashe tashen hankula 231 da aka samu a Kudu maso Kudu wanda suka kunshi matsalar kungiyoyin asiri da tsageru, mutane aƙalla 336 aka kashe tare da sace wasu 295.
Makamantan waɗannan matsaloli daɗi da fafutukan ƴan aware da kashe-kashe ya laƙume rayukan ƴan Najeriya 310, kana an yi garkuwa da 212 a Arewa maso Gabas.
A Kudu maso Yamma kuwa kungiyoyin asiri, ‘yan fashi da sauran nau’ukan ƴan tayar da ƙayar baya sun kashe fararen hula akalla 172, yayin da aka sace wasu 225.
Manyan hare-haren ta'addanci a mulkin Tinubu
Watanni uku bayan Tinubu ya shiga ofis, aka girgiza gwamnatinsa da kisan sojoji 36 yayin da suka yi yunkurin kai ɗauki a kauyukan jihar Neja ranar 14 ga watan Agusta.
A wannan rana, ƴan ta'adda karkashin jagorancin Dogo Gide suka harbo wani jirgin soji da ke aikin ceto, duk da cewa rundunar sojin saman Najeriya ta ce hatsari ne.
Bayan watanni uku, ‘yan Najeriya sun wayi gari da labari mai ban tsoro daga kananan hukumomin Bokkos da Mangu a jihar Filato inda aka kashe mutane sama da 100 a jajibirin Kirsimeti.
A watan Maris, 2023, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka sace dalibai 137 daga makarantun firamare da sakandire a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Ɗaliban sun shaƙi iskar ƴanci makonni biyu bayan faruwar lamarin, wasu rahotanni sun ce an biya kuɗin fansa duk da ba a bayyana adadin kuɗin ba.
...An rasa sojoji a zamanin Tinubu
A wannan watan, wasu matasa suka kashe sojoji 15 da suka kunshi Manjo biyu, Kyaftin daya da wasu jami'ai 12 na bataliya ta 181 a kauyen Okuama da ke jihar Delta.
Sojojin na gudanar da aikin dawo da zaman lafiya a tsakanin kuyuka biyu da ke faɗa da juna, Okuama da Okoloba a karamar hukumar Bomadi, lokacin da makasan suka kewaye su.
Tinubu ya ɗauki hanyar cika alƙawarinsa?
Duk da cewa Najeriya ta yi asarar rayuka da dama a cikin wa'adin shekara ɗaya da muke nazari a kai, amma su ma ƴan ta'addan ba su tsira ba.
Bayanan da ACLED ta tattara sun nuna cewa samamen sojoji da kuma yaƙar juna tsakanin ƙungiyoyin ƴan ta'adda sun yi ajalin ƴan bindiga 4,165 tun bayan hawan Tinubu.
Da yake jawabi a taron yaye ɗalibai a jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUS), mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana hanyoyin da gwamnati ke bi wajen kawo karshen matsalar tsaro.
"A bangaren yaƙi, sojoji na ci gaba da kai samame kan kungiyoyin masu tada kayar baya kamar Boko Haram da 'yan bindigan da suka addabi Arewacin Najeriya."
Mista Ribadu ya kara da cewa irin wannan samamen hadin-gwiwa tsakanin jami'an tsaron ya kai ga halaka manyan ‘yan ta’adda irinsu Ali Kawaje.
Masana sun ce akwai sauran aiki
Sai dai wani masani kan harkokin tsaro, Kabir Adamu, ya ce har yanzu shugaban kasar bai magance tushen rashin tsaron ba, duk kuwa da zuba hannun jari a fannin.
Mista Adamu, wanda shi ne shugaban rundunar leken Asiri na Beacon mai zaman kanta, ya yaba da yadda sojoji ke yaki da ‘yan ta’adda.
Ya ce yaɗuwar makamai, shaye-shaye, sakin iyakoki sakaka, rashin adalci da gaza aiwatar da tsare-tsaren da suka dace su ne tushen matsalar tsaron wanda har yanzun aka kasa shawo kansu.
Masanin ya shawarci gwamnonin jihohin Najeriya su shiga a dama da su a tsare-tsaren tsaron ƙasa.
Gwamna Raɗɗa ya nemi taimakon Tinubu
A wani rahoton kuma Gwamnatin Katsina tayi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taimaka domin a dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasiru Ɗanmusa ya ce a yanzu ƴan bindiga sun fara kai hari da miyagun makamai.
Asali: Legit.ng