An Hallaka Mutum 2 Yayin Gwabzawar 'Yan Sanda da Masu Garkuwa da Mutane a Kogi

An Hallaka Mutum 2 Yayin Gwabzawar 'Yan Sanda da Masu Garkuwa da Mutane a Kogi

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kogi sun samu nasarar hallaka wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
  • Ƴan sandan sun hallaka masu garkuwa da mutanen ne bayan sun yi arangama da ba-ta-kashi a dajin Ankumi da ke Kogi
  • Bayan fafatawar ƴan sandan sun ƙwato kayayyaki a hannun masu garkuwan da mutanen yayin da suka raunata mutum ɗaya wanda ya tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Jami’an tsaro na ƴan sanda sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Kogi.

Jami'an ƴan sandan sun kuma ƙwato kayayyaki a hannun waɗanda ake zargin bayan sun yi musayar wuta.

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane a Kogi
'Yan sunda sun hallaka masu garkuwa da mutane yayin artabu a jihar Kogi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, jigida guda biyu da kuma harsasai guda biyu, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

"Mun shirya tsaf," 'Yan sanda sun ƙara ɗaukar mataki kan rigimar sarautar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a birnin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Ƴan sanda sun sheƙe masu garkuwa da mutane

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa an samu nasarar hallaka masu garkuwa da mutanen ne bayan an samu bayanan sirrri kan motsinsu a cikin daji.

Ya bayyana cewa an samu bayanan ne a ranar 27 ga watan Mayun 2024 inda suka nuna cewa mutanen su uku suna ɗauke da makamai a dajin Ankumi.

"Nan take babban jami’in ƴan sanda na reshen Obajana, CSP Oguche Richard ya haɗa tawagarsa ta sintiri tare da haɗin gwiwar ƴan banga na Fulani inda suka garzaya zuwa yankin."
"Da ganin tawagar, masu garkuwa da mutanen sai suka buɗe wuta inda nan da nan jami'an tsaron suka mayar da martani."

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: 'Yan sanda sun bankado shirin tada tarzoma a Kano, sun yi gargadi

"Sakamakon fifikon kayan aikin ƴan sandan, sun yi nasarar hallaka mutum biyu daga cikinsu yayin ɗayan ya tsere da raunukan harsashin bindiga."
"Kayayyakin da aka ƙwato daga wurin sun haɗa da bindigairar AK 47 guda ɗaya, jigida guda biyu da harsasai guda biyu. Ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ɗayan wanda ake zargin da ya tsere."

- SP William Aya

Ƴan sanda sun cafke ɗan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Muhammad Bello.

Jami'an ƴan sandan sun cafke ɗan bindigan ne a wani samame da suka kai garin Kidandan da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng