"Ƴan Bindiga Sun Fara Kai Hari da Manyan Bindigu," Gwamna Radɗa Ya Tura Saƙo ga Tinubu
- Gwamnatin Katsina ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taimaka domin a dawo da zaman lafiya a faɗin jihar
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasiru Ɗanmusa ya ce a yanzu ƴan bindiga sun fara kai hari da miyagun bindigu
- Ya kuma jaddada cewa Gwamnatin Dikko Raɗɗa ba za ta nemi sulhu da ƴan bindiga ba, za ta ci gaba da yaƙarsu har sai zaman lafiya ya dawo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta roki gwamnatin tarayya ta kawo ɗauki domin magance matsalar tsaro a jihar.
Gwamnatin ta jaddada buƙatar gwamnatin tarayya ta samar da kayan aiki masu inganci ga jami'an tsaron jihar domin su ci gaba da yaƙi da ƴan bindiga.
'Yan bindiga sun gawurta a Katsina
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasiru Ɗanmusa ne ya yi wannan kira ranar Litinin da daddare, kamar yadɗa Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubi ya kawo wa Katsina agaji ne jim kaɗan bayan taron majalisar tsaro na gaggawa karkashin jagorancin Gwamna Raɗɗa.
Gwamnati ta gano shirin ƴan bindiga
Ya ce gwamnatin jihar ta gano cewa ‘yan bindigar da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jihar, yanzu suna amfani da manyan makamai irinsu RPG.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Katsina ta kudiri aniyar ci gaba da tunkarar ƴan bindigar har sai zaman lafiya ya dawo a dukkan sassan jihar.
Ya kuma bayyana cewa ba za a nemi sulhu da ƴan ta'addan ba musamman a wannan lokacin da aka rage masu ƙarfi.
Ɗanmusa ya yabawa yadda aka ƙara samun haɗin kai tsakanin jami'an tsaro da gwamnati, inda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin bayan ƴan bindiga.
Ya ce:
"Muna da kwarin guiwa game da jami’an tsaro kuma muna aiki tare a matsayin ‘yan uwa wanda hakan ma ya ba mu dama da nasarori a yaki da ƴan bindiga a jihar.
Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba kuma gwamnanmu ya shirya tsaf don magance matsalar rashin tsaro, shi ya sa batun tsaro shi ne abu na ɗaya, na biyu da na uku da ya fi bai wa fifiko."
DHQ ta kalubalanci Dikko Radɗa
A wani rahoton kuma hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi martani kan zargin da gwamnan jihar Katsina ya yi na cewa wasu gurɓatattun sojoji na haɗa baki da ƴan bindiga.
DHQ ta ƙalubalanci gwamnan da ya kawo hujjojin da za su tabbatar da zargin da ya yi kan jami'an rundunar sojojin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng