Masarautun Kano: Lauyoyin Arewa Sun Ba Abba Wa’adin Awa 48 Ya Tsige Sarki Sanusi II

Masarautun Kano: Lauyoyin Arewa Sun Ba Abba Wa’adin Awa 48 Ya Tsige Sarki Sanusi II

  • An ba gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wa'adin awa 48 ya janye nadin da ya yiwa Sarki Muhammadu Sanusi II
  • Kungiyar lauyoyin Arewa wadanda suka ba da wa'adin sun yi barazanar daukar matakin shari'a idan Abba ya gaza cika sharadin
  • Lauyoyin sun yi ikirarin cewa mayar da Sarki Sanusi II ya sabawa tsarin mulki da kuma sabawa al'adar masarautar Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar lauyoyin Arewacin Najeriya sun ba gwamnan Kano, Abba Yusuf wa'adin awa 48 ya janye nadin da ya yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II.

Lauyoyi sun nemi Abba ya tsige Sarki Sanusi II
Kano: Lauyoyin daga Arewa sun ba Gwamna Abba wa'adi ya tsige Sarki Sanusi II.
Asali: Original

Lauyoyin, wadanda suka bayyana kan su a matsayin 'kungiyar lauyoyin Arewa', sun ba da wa’adin ne a wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta roki sarkin Kano 15 Aminu Ado Bayero ya rungumi kaddara

Lauyoyi sun soki dawo da Sarki Sanusi II

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lauyoyin sun yi ikirarin maida Sarki Sanusi II "ya sabawa tsarin mulki" kuma "ya sabawa al'ada da gudanarwar masarautar Kano."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Umar Sadik Abubakar, shugaban kungiyar ya ce tsige Sarki Sanusi II da aka yi a 2020 an yi ne bisa doron doka da kuma al'adun masarautar Kano.

A cewarsa, mayar da Sarki Sanusi II kan mukaminsa "zai haifar da hargitsi tare da lalata tsarin doka" a jihar.

Sanusi II: Lauyoyi za su yi karar Abba

Abubakar ya zargi Abba da kin mutunta hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yi na hana gwamnan dawo da Sarki Sanusi II kan mulki, in ji rahoton Daily Post.

Lauyan ya ce, umarnin da Gwamna Yusuf ya karbo daga babbar kotun jihar Kano da nufin yin watsi da hukuncin kotun tarayya cin mutuncin babbar kotun ne.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kamar Sanusi II, shi ma Aminu Bayero ya yi zaman fada a Nassarawa

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan har gwamnan ya gaza janye nadin, za a tilasta mata daukar “dukkanin matakan shari’a” domin kare fannin shari’a da muradun mutanen Kano.

Kotu ta yi hukunci kan sarautar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Kano a jiya Litinin ta dakatar da sarakuna biyar da aka rusa a jihar daga gabatar da kansu matsayin sarakuna.

Haka zalika, kotun ta umarci rundunar 'yan sandan jihar da ta karbe ikon gudanarwar masarautar Nasarawa daga hannun tsohon sarkin Kano na 15, Aminu Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.