Kungiyar Arewa ta Roki Sarkin Kano 15 Aminu Ado Bayero ya Rungumi Kaddara
- Kungiyar kwararru a Arewa ta NPF ta roki sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero kan ya karbi kaddarar cire shi daga sarauta da gwamnati ta yi
- Darakta Janar a kungiyar Usman Yusuf ne ya yi rokon ta cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, inda ya ce sarkin na 15 ya yi hakuri shi zai fi
- Har yanzu ana dambarwar masarautar Kano domin Sarki Aminu Ado Bayero har yanzu yana jihar tare da zaman fada a gidan Sarki a Nassarawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar kwararrun ma'aikata a Arewacin Najeriya (NPF) ta roki Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rungumi kaddara kan sauke shi da gwamnati ta yi.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rushe masarautun jihar biyar tare da nada sabon sarki.
A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce akwai bukatar tabbatar da zaman lafiya saboda haka ta roki sarkin ya hakura, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NPF: A yiwa Sarki Sanusi II mubayawa
Kungiyar kwararrun ta Arewacin kasar nan, ta nemi 'yan siyasa da sauran jama'a su yiwa Sarki Muhammadu Sunusi II mubayawa.
A sanarwar da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun darakta janar dinta, Usman Yusuf, ta bukaci a tabbatar da zaman lafiya.
Usman Yusuf ya kara da cewa kamata ya yi Sarki na 15 ya nuna dattako wajen rungumar lamarin a matsayin kaddara.
Masarauta: Jigon APC ya nemi taimakon Tinubu
Daya daga magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Abdul-Majid Danbilki Kwamanda ya roki shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki cikin dambarwar masarautar Kano.
Vanguard News ta wallafa cewa Danbilki kwamanda na ganin bai kamata gwamnatin Tinubu ta rufe idanu har gwamnatin Kano ta tsige sarakuna ta nada sabo ba duk da umarnin kotu.
Gaskiya ta bayyana kan dawowar Aminu Ado
A baya mun kawo muku labarin yadda sarkin Dawaki, Aminu Babba Danagundi ya bayyana yadda aka dawo da sarkin kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Ya musanta zargin cewa ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro karkashin Nuhu Ribadu ne ya bayar da jiragen dawo da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng