Ana Tsaka da Cin Kwakwa, Majalisa Ta Sauya Taken Najeriya, Ta Fadi Amfaninsa

Ana Tsaka da Cin Kwakwa, Majalisa Ta Sauya Taken Najeriya, Ta Fadi Amfaninsa

  • Yayin da ƴan Najeriya ke fama da halin kunci, Majalisar Tarayya ta amince da dawo da tsohon taken kasar da aka bari a baya
  • Kudirin wanda Sanata Tahir Monguno daga jihar Borno ya gabatar ya tsallake karatu na uku a majalisar a yau Talata
  • Legit Hausa ta tattauna da wasu matasa kan wannan sabon taken Najeriya da Shugaba Bola Tinubu ya kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta tabbatar da kudirin dawo da tsohon taken Najeriya domin kara kishin ƙasa.

Majalisar ta amince da kudirin bayan ta tsallake karatu na 3 a yau Talata 28 ga watan Mayu.

Majalisa ta amince da sauya taken Najeriya
Majalisar Dattawa ta amince da dokar dawo da tsohon taken Najeriya tare da sauya wanda ake yi yanzu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Majalisa ta amince da sauya taken Najeriya

Kara karanta wannan

Bayan Najeriya, ga cikakken jerin kasashen Afirka 7 da suka canza taken kasa

Tahir Monguno daga jihar Borno shi ya gabatar da kudirin inda ya ce wannan mataki ne mai matukar muhimmanci, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon taken Najeriya "Nigeria, We Hail Thee" zai maye gurbin "Arise O Compatriots" da ake amfani da shi a yanzu, Channels TV ta tattaro.

Yayin gabatar da kudirin, Monguno ya ce kwamitin shari'a ya ki amincewa da Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi kan cewa lamarin yana bukatar dogon nazari.

Majalisar dokoki ta tabbatar da kudirin

A makon da ya gabata ne, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar ta dawowa tsohon taken Najeriya da ake yi.

Mafi yawan mambobin Majalisun sun goyi bayan kudirin yayin da ake tattaunawa a kai a makon da ya gabata.

Mambobin sun bayyana cewa wannan mataki zai karawa ƴan Najeriya kishin kasa fiye da taken kasar da ake yi yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ba da kwana 3 a haddace sabon taken Najeriya, an fadi fa'idar hakan

Legit Hausa ta tattauna da wasu matasa

Legit Hausa ta tattauna da wasu matasa kan wannan sabon taken Najeriya da Tinubu ya kawo.

Wani shugaban kungiyar matasa a Gombe, Muhammad Khamis ya ce tabbas an rasa abin da ya kamata a ba kulawa a Najeriya.

"Abin takaici ne yadda ake fama da halin kunci ace an kawo irin wannan kudiri a dai-dai wannan lokaci."

- Muhammad Khamis

Wani malamin makaranta, Muhammad Yakubu ya ce a yanzu haka an fara matsawa dalibai da malamai su koyi sabon taken Najeriya.

Ya ce mutane suna cikin wani hali musamman rashin wuta a Arewa maso Gabas shi ne babban damuwa amma ana maganar taken Najeriya.

Ya bukaci gwamnati ta mai da hankali kan abin da zai kawo dauki ga al'umma domin inganta rayuwarsu.

Tinubu zai yi jawabi a majalisun tarayya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu zai yi jawabi a majalisun Tarayya guda biyu a gobe Laraba 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki kan korar daraktoci da manyan ma'aikata a bankin CBN

Tinubu zai yi wa majalisun jawabi a tare game da nasarar dimukradiyya shekaru 25 da kuma nasarar kasancewar majalisun ba tare da matsala ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel