Bidiyon Jami'an Tsaro Sun Tare a Fadar Nasarawa Duk da Umarnin Kotu Kan Aminu Ado

Bidiyon Jami'an Tsaro Sun Tare a Fadar Nasarawa Duk da Umarnin Kotu Kan Aminu Ado

  • An gano tulin jami'an sojoji da ƴan sanda jibge a kusa da fadar Nasarawa inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yake
  • A cikin wani faifan bidiyo an gano yadda jami'an tsaro suka yi wa wurin tsinke da motocinsu domin tabbatar da tsaro a wurin
  • Wannan na zuwa ne bayan umarnin babbar kotun jihar kan tuge Aminu Ado Bayero karfi da yaji daga fadar Nasarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da kotu ta ba da umarnin tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, an tsaurara tsaro a fadar Nasarawa.

An gano jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji na ƴan sanda sun ja daga domin tabbatar da tsaron karamar fadar da ke Kano.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga ɗimuwa bayan jin harbe harbe a fadar da Aminu Ado Bayero yake

Jami'an tsaro sun cika fadar Nasarawa da Aminu Ado ya ke
An jibge jami'an tsaro a fadar Nasarawa bayan umarnin kotu kan Aminu Ado Bayero. Hoto: @Super_Joyce1/DSS.
Asali: Twitter

Kano: Jami'an tsaro sun cika fadar Nasarawa

A cikin wani faifan bidiyo da TheCable ta wallafa a shafin X a yau Talata 28 ga watan Mayu, an gano motocin jami'an tsaron a girke a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun jihar Kano ya umarci fitar da Aminu Ado Bayero da karfi daga fadar Nasarawa a jihar Kano.

Kotun ta umarci kwamishinan yan sanda ya tabbatar da bin dokar tare da daukar mataki kan Aminu Ado Bayero wanda aka tsige shi.

Har ila yau, gwamnatin jihar Kano ta nemi taimakon Shugaba Bola Tinubu wurin fitar da Sarkin Kano na 15 domin samun zaman lafiya.

Kano: Abba kabir ya tube sarakuna 5

Gwamna Abba Karbi na jihar ya tube sarkin Kano na 15 da sauran sarakuna hudu da ke jihar wanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira a 2019.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Daga bisani Aminu Ado ya shigo Kano inda ya wuce fadar Nasarawa a ranar Asabar 25 ga watan Mayu kwanaki biyu bayan rasa sarautarsa.

Shigowarsa ke da wuya, Gwamna Abba Kabir ya bukaci jami'an tsaro su cafke shi kan zargin neman ta da husuma da kawo rashin zaman lafiya.

An jiyo harbe-harbe a fadar Nasarawa

Kun ji cewa wasu mutanen yankin fadar Nasarawa sun tabbatar da jin harbe-harbe a yankin wanda ke fitowa daga karamar fadar a daren jiya.

Wasu da ke kusa da wurin sun tabbatar da jin harbe-harben inda suke zargin an yi hakan ne domin dakile kokarin tuge Aminu Ado daga fadar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.