Kaduna: Rashin Tsaro Ya Munana, Ƴan Bindiga Sun Gindayawa Manoma Sharuɗan Shiga Gona

Kaduna: Rashin Tsaro Ya Munana, Ƴan Bindiga Sun Gindayawa Manoma Sharuɗan Shiga Gona

  • Ƴan bindiga a jihar Kaduna sun gindaya sharuda kan wasu manoma domin ba su damar yin noma a bana
  • Maharan sun bukaci kowane manomi a wasu ƙauyukan jihar ya nemo N100,000 a matsayin hukunci domin basu damar yin noma ba tare da matsala ba
  • Ƴan bindigan na zargin wasu a ƙauyukan Unguwar Jibo da Nasarawa da tona musu asiri a wurin sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Wasu manoma a jihar Kaduna sun shiga halin kunci bayan sabon umarni da ƴan bindiga suka ba su.

Maharan sun umarci manoma a Unguwar Jibo da Nasarawa da ke karamar hukumar Kachia su nemo N100,000 domin samun damar yin noma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan biyan N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Yan bindiga sun ba manoman Kaduna sabon sharadi kan noman bana
Manoman Kaduna suna cikin zullumi bayan umarnin ƴan bindiga na biyansu N100,000. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Musabbabin ƙaƙaba sharadin ƴan bindiga ga manoma

Miyagun suka ce wannan shi zai ba su damar barinsu su yi noma a matsayin hukuncinsu kan tona musu asiri a wurin jami'an sojoji da suke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani da ya bukaci boye sunansa ya fadawa Daily Trust cewa akwai wasu ƙauyuka uku da suma aka bukaci su kawo N100,000 kowa daga cikinsu.

Ya ce ƙauyukan sun hada da Hayin Dam da Dogon-Daji da Gidan-Makeri a karamar hukumar Kagarko.

Kaduna: Ƴan bindiga sun ba manoma umarni

Majiyar ta ce bayan N100,000 da aka bukata, ƴan bindiga sun umarci su rika siya masu abinci da magani bayan mako biyu domin cika sharudan barinsu suyi noma a yankunan.

Wani shugaban al'umma a yankin da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar da hakan inda ya ce wannan mataki ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki ƴan majalisa 5, sun buɗe masu wuta a Arewacin Najeriya

Ya bukaci gwamnati da ta kawo musu daukin gaggawa da karin jami'an tsaro domin kare su daga sharrin wadannan miyagu.

Ƴan bindiga sun hallaka daliban Jami'a

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi ajalin daliban Jami'ar jihar Kogi da suka sace a farkon watan Mayun nan da ake ciki.

Rundunar ƴan sanda a jihar Kogi ita ta tabbatar da haka ga manema labarai inda ta ce ta baza jami'anta domin ceto sauran daliban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.