Sarki Na 15 Aminu Ado Bayero Ya Fito Daga Fadar Sarkin Kano, Bidiyo Ya Bayyana
- Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 ya fito daga karamar fadar da ke Nassarawa da yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Mayu
- Tun ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu aka fara taƙaddama kan sarautar Kano bayan Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II
- Sai dai har yanzun mutane na son sanin wanene sarki yayin da Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama a ƙaramar fadar sarkin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan kujerar sarauta, Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 ya fito daga ƙaramar fadar sarki da ke Nassarawa.
A wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Aminu Ado ya fito daga fadar ne a kan doki kuma nan take magoya bayansa suka fara murna da kai gaisuwa.
Kamar yadda jaridar Leadership ta kawo a rahotonta, magoya bayan Aminu Ado Bayero sun ɓarke da shewa tare da miƙa gaisuwa yayin da basaraken ya riƙa amsawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai har kawo yanzu babu tabbacin ko Aminu Bayero ya baro fadar ne gaba ɗaya ko kuwa ya ɗan fito ne da nufin zai sake komawa.
Gwamnan Kano, Abba ya maido Sanusi II
Legit Hausa ta tattaro muku cewa a ranar Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan karaga.
Gwamnan ya miƙa wa sarkin takardar shaidar kama aiki a wani taro da aka shirya a fadar gwamnati da ke cikin birnin Kano.
Tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na yanzu, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsige Sanusi daga kujerar sarauta a shekarar 2020.
Sai dai dawo da Sanusi II da Gwamna Abba ya yi ya zo da tangarɗa bayan Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama a karamar fadar sarki.
Gwamnan Kano ya ba da umarnin a kama Aminu Ado, amma jami'an tsaro suka ce ba za su bi umarni ba saboda kotu ta hana naɗin Sanusi II.
Gwamna Abba ya roƙi Tinubu alfarma
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf Kabir Yusuf ta bukaci Bola Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar Kano
Mataimakin gwamnan jihar wanda ya yi wannan kiran ya buƙaci Tinubu da ya taimaka ya fitar da Aminu Ado Bayero daga Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng