'A Rabu da Fetur,' Jagora a APC Ya ba Tinubu Lakanin da Najeriya Za Ta Samu Kudi
- Jagora a jam'iyyar APC ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dabarun habaka tattalin arzikin Najeriya ba tare da man fetur ba
- Olatunbosun Oyintoloye wanda jigo ne a jam'iyyar reshen jihar Osun ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan albarkatun teku
- Ya bayyanawa manema labarai a Osogbo cewa an gano za a iya samun dala biliyan 20 duk shekara daga bangaren tare da samar da aiki miliyan 2
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun-Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintoloye ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan dabarun samun karin arziki a Najeriya.
Ya bayyana dabarun a Osogbo yayin tattaunawa da manema labarai, inda ya ce ya kamata a rage dogaro da man fetur.
The Cable ta wallafa cewa jigon jam'iyyar ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan albarkatun da ake samu a teku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Za a samu $20b duk shekara,' Oyintoloye
Jagora a jam'iyya mai mulki na APC ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa samar da ma'aikatar kula da albarkatun teku da arzikin da ake samu a bangaren.
Ya ce ministan ma'aikatar, Gboyega Oyetola ya gano cewa bangaren zai rika samar da $20b duk shekara.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya wallafa cewa Oyintoloye na ganin za a iya kara habaka bangaren domin rage dogaro da man fetur.
Ya kara da cewa amma dole sai an samar da tsarin kudi da samar da kudaden gudanar da wasu ayyukan kamar bunkasa yawon bude ido a bangaren tekunan kasar nan.
Rance daga CBN: Gwamnati ta fara bincike
A baya mun ruwaito muku cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta jagoranci binciken rancen da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ciwo daga CBN.
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ci bashin Naira tiriliyan 23 domin gudanar da wasu ayyuka, lamarin da gwamnati ta ce za ta biya amma za ta bincika.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng