Sarautar Kano: Magoya Bayan Tsohon Sarki Aminu Bayero Sun Gudanar da Sallar Al-Qunut
- Magoya bayan sarakuna biyar da gwamnatin jihar Kano ta rattaba hannu aka tube rawunansu sun gudanar da Sallar Al-Qunut
- An ruwaito cewa an gudanar da sallar tare da yin addu'o'i a kusan dukkanin masarautun da abin ya shafa da fatan maido da sarakunan
- Hotuna da bidiyo sun nuna yadda magoya bayan tsofaffin sarakunan suka yi gangami tare da mika lamuransu ga Allah kan lamarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Magoya bayan tsohon sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, sun gudanar da addu’a ta musamman ga sarkin kan Allah ya kwato masa hakkinsa.
Dandazon magoya bayan sun taru a wani fili inda suka gudanar da Sallar Al-Qunut kan rikicin da ya mamaye masarautun jihar.
Tijjani Sani Amsko ya wallafa bidiyon yadda al'umar suka gudanar da sallar a shafinsa na Facebook. An ce an gudanar da sallar a wajen fadar Aminu Bayero da ke Nassarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi Sallar Al-Qunut a Rano
Haka zalika, an gudanar da makamanciyar wannan Sallar Al-Qunut din a karamar hukumar Rano, inda mutane suka yi addu'o'i kan Allah ya dawo da sarakunan Kano da aka rusa.
Abdullahi Suleman Ɗambatta ya wallafa hotunan yadd aka gudanar da sallar daga masarautar Rano a shafinsa na Facebook.
Kalli hotunan a kasa:
An yi Sallar Al-Qunut a Gaya
A yankin masarautar Gaya ma, dandazon mutane ne suka yi sahu-sahu tare da gabatar da Sallar Al-Qunut da yin addu'o'i kan Allah ya dawo da sarakunan Kano biyar da aka kora.
Aminu Jan Mutum ne ya wallafa hotunan yadda gangamin sallar ya gudana a shafinsa na Facebook, kalla a kasa.
Zanga-zanga ta mamaye Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa zanga-zanga ta barke a wasu na jihar Kano inda masu zanga-zangar ke nuna adawa da maido da Muhammadu Sanusi kan sarautar Kano.
An gudanar da wannan zanga-zangar a Gaya, Nassarawa da wasu sassa na sauran masarautun da gwamnatin jihar ta rusa a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng