Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Karbar Umurnin Kotu Kan Sauke Aminu Ado Bayero

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Karbar Umurnin Kotu Kan Sauke Aminu Ado Bayero

  • Ana cigaba da samun dambarwa a jihar Kano biyo bayan sauke mai martaba Aminu Ado Bayero da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
  • Wani basarake a jihar ya kalubalanci hukuncin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zartar kan sarakunan jihar a kotun tarayya da ke Kano
  • A farko gwamantin ta ce ba ta samu umurnin kotu kan dakatar da sarakunan ba amma a yau Litinin, ta tabbatar da karɓar umurnin kotun

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da samun umurnin kotun tarayya kan dakatar da tsige sarakunan Kano da gwamna Abba ya yi.

Masarautu
Gwamnatin Kano ta karbi takarda daga kotu kan rusa masarautu. Hoto: Masarautar Kano| Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

BBC Hausa ta ruwaito cewa a yau Litinin, 27 ga watan Mayu ne kwamishinan Shari'a na jihar ya tabbatar da karbar umurnin kotun.

Kara karanta wannan

Rikicin masarautar Kano: Sheikh Dahiru Bauchi ya aika muhimmin sako ga Abba

Umurnin kotun yana nuni da cewa gwamnatin za ta dakatar da nada Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 ta kuma dawo da masarautun da ta rushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe umurnin kotu ya riski gwamantin Kano?

Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Isa Dederi ya tabbatar da cewa a yau Litinin, 27 ga watan Mayu da misalin karfe 10:00 na safe umurnin kotun ya riske su.

Ya kuma kara da cewa wani ma'aikacin kotun gwamantin tarayya da ke Kano ne ya kawo masa takardar a yau.

Wane mataki gwamnatin Kano za ta dauka?

Kwamishinan shari'ar ya ce takardar ta zo musu ne bayan sun riga sun kammala nada sabon sarki da rusa masarautun jihar.

Amma duk da haka ya ce za su bayyana a gaban kotun tare da mika nasu takardun su ga hukuncin da kotun za ta yanke.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fusata da dabi'un gwamnonin Najeriya, ta maka su a Kotun Koli

Aminu Ado Bayero ya dawo Kano

Saboda umurni da kotun ta yi ne Aminu Ado Bayero ya dawo Kano a daren Juma'a yana kiran kansa a matsayin sarki duk da cewa gwamnatin ta sanar da sauke shi.

A yanzu haka dai Aminu Ado Bayero yana zaman fada kamar yadda Muhammadu Sanusi II yake zaman fada a wani wuri na daban.

Malamin addini ya yi kira kan sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa shahararren malamin addinin Musulunci, Lawal Triumph ya yi jawabi kan yadda aka tashi da sarakuna biyu a jihar Kano.

Sheikh Lawal Triumph ya yi kira na musamman ga hukumomin jihar domin daukan mataki kan lamarin saboda kaucewa tashin rikici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel