Dambarwar Sarauta: 'Babu Mai Tirsasa Mu,' Mataimakin Gwamnan Kano ya yi Martani
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta dauki matakin rushe masarautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira bisa doron shari'a
- Mataimakin Gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya bayyana haka a tattaunarsa da manema labarai a safiyar yau Litinin
- Ya bayyana cewa babu wanda ya isa ta zare musu idanu kan matsayar da suka dauka na sake nada sarki Muhammadu Sanusi II sarki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Dambarwar Kano na ci gaba da daukar dumi, inda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce babu yadda zai yi mata dole kan soke masarautun Kano biyar.
Mataimakin Gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce suna kan bakarsu na dawo da Malam Muhammadu Sanusi II karagarsa.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa mataimakin Gwamnan na wannan batu biyo bayan dambarwar da ta dabaibaye batun masarautar Kano a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Alhamis ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar da ta rushe masarautun Kano biyar da Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira.
Rushe Masarautu: ‘Gwamnati ta bi doka ,’ Gwarzo
Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya bayyana cewa sun bi doka yadda ya kamata kafin rushe masarautun jihar, kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.
A kalamansa:
”Jihar Kano ta dauki matakin ne ta hanyar shari’a yadda ta dace. Babu wanda zai bude mana ido saboda mun yanke hukuncin da ya dace da mutanenmu.”
”Abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano domin ci gaban.”
Tun bayan nada sabon sarki a jihar aka samu martani daga sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya ki amincewa da hakan.
Sarki Bayero ya dawo Kano ya tare a gidan sarki dake Nassarawa, lamarin da gwamnatin ke kallo a matsayin takalar rigima.
Rikicin masarauta: Gwamnatin Kano ta nemi agaji
A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo musu agaji cikin gaggawa.
Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya nemi daukin domin hana jihar daga afkawa rikici biyo bayan nadin sabon sarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng