Shahararren Malamin Kano Ya Yi Magana Bayan an Tashi da Sarakuna 2 a Gari

Shahararren Malamin Kano Ya Yi Magana Bayan an Tashi da Sarakuna 2 a Gari

  • Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawal Triumph ya yi jawabi kan yadda aka tashi da sarakuna biyu a jihar Kano
  • Sheikh Lawal Triumph ya yi kira na musamman ga hukumomin jihar domin daukan mataki kan lamarin saboda kaucewa rikici
  • Ya kuma bayyana cewa yadda ba a sarki biyu a fada guda daya haka ba a hada Allah SWT da wani a cikin sarautarsa da bauta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shahararren malamin addinin Muslunci a jihar Kano, Sheikh Lawal Abubakar Triumph ya yi jawabi kan yadda aka tashi da sarakuna biyu a Kano.

Sarakuna biyu a Kano
Malamin addini ya yi kira kan samar da sarki daya a Kano. Hoto: Masarautar Kano|Malam lawal Abubakar Triumph
Asali: Facebook

Malamin ya yi jawabin ne a wani bidiyon da Alhassan Mai Lafiya ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

"Na karbi kaddara": Sarkin Gaya ya yi magana bayan gwamnatin Kano ta tube rawaninsa

A cikin bidiyon, malamin ya yi kira na musamman ga hukumomin jihar Kano domin daukan matakin gaggawa kafin lamarin ya rincaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki 2: Triumph yana so doka tayi aiki

Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa ba ya kamata a samu sarakuna biyu a gari daya idan ana son samun hadin kai da zaman lafiya.

A karkashin haka babban malamin ya ce ya kamata doka ta yi aiki a kan lokaci wajen ganin hakan bai cigaba ba. Ga abin da yake cewa:

"Yanzu mu a Kano mun samu kanmu a wani yanayi, muna cikin Kano mutane biyu kowa na da'awar shi sarki ne. Ba zai yiwu ba."
"Dole ne doka da oda ta yi abin da za ta yi a samu guda daya. Sarki biyu ba sa yiwuwa a masarauta guda daya,"

- Sheikh Lawal Triumph

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

Sarki 1: Haka lamarin yake a fadar Allah

Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa kamar yadda ba a samun sarki sama da daya a fadar duniya, haka Allah ma shi daya ne.

Ya kara da cewa hakan yana nuna bacin tunanin masu zaton za a iya samun abin bauta na gaskiya sama da Ubangiji Madaukaki.

Majalisa ta tsige sarkin Kano

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Kano ya ce kudirin dokar da suka yi ya soke sarakunan da Abdullahi Ganduje ya naɗa.

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na cikin waɗanda wannan matakin ya shafa tare da sauran sarakuna huɗu da Ganduje ya nada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel