"Ba Mu Cancanci Haka Ba": Masarautar Bichi Ta Magantu Yayin da Ta Yabi Jami'an Tsaro
- Masarautar Bichi ta yabawa kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a wurin tabbatar da zaman lafiya a Kano
- Masu ruwa da tsaki a masarautar sun kuma yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nuna adalci da bin doka
- Masarautar ta ce babu wani laifi da ta yi ga majalisar jihar ko gwamnatin Kano da suka cancanci wannan hukunci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Masarautar Bichi a jihar Kano ta magantu kan matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka kan masarautun.
Masu ruwa da tsaki a masarautar sun yabawa jami'an tsaro da kuma bangaren shari'a kan dogewa wurin tabbatar da kundin tsarin mulki.
Sanarwar da masarautar Bichi ta fitar
Nasiru Ado Bayero shi ke jagorantar masarautar kafin rusa su a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wasu daga cikin dattawan masarautar 39 suka sanyawa hannu.
"Masarautar Bichi tana godiya matuka ga bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro kan yadda suka tsaya wurin tabbatar da bin doka a wannan lamari."
"An tauyewa mutanen Bichi da masarautarta hakkinsu amma kokarin jami'an tsaro da bangaren shari'a ya dakile tashin hankali a masarautar da ma sauran masarautun guda hudu."
"Babu tantama dukkan masarautun guda hudu sun samu ci gaba a shekaru takwas da suka wuce ba tare da aikata wani laifi da suka cancanci wannan hukunci daga majalisa da kuma gwamnatin jihar ba."
- Masarautar Bichi
Har ila yau, masu ruwa da tsakin sun godewa Shugaba Bola Tinubu kan nuna adalci da bin doka a lamarin, cewar Daily Post.
Masu ruwa da tsakin masarautar Bichi
1. Mal Bello Salisu
2. Alh Uba Kunchi
3. Alh Sule Mu’azu Kunchi
4. Mal Muhammad Garba Yusuf
5. Alh Mudassir Ado Kunchi
6. Alh Tukur Sani Kwa
7. Mal Kabiru Muhammad
8. Alh Musa Zangon Mata
9. Sani Alasan Dawaki
10. Alh Ado Rabiu Danbayero
11. Alh Mohd Abba Danbatta
12. Alh Yahaya Nuhu
13. Alh Magaji Sani Maidaji
14. Alh Ibrahim Nuhu Amasaye
15. Alh Muntari Sale
16. Alh Danasabe Makoɗa
17. Alh Rabiu Abubakar Makoɗa
18. Mal Yusuf Yusuf Lawan
19. Alh Suleiman Ahmed Auwal
20. Hon Ibrahim Damisawa
21. Alh Babangida Mansur Kunya
22. Alh Murtala Rufa’i
23. Mal Musa Mai Azara
24. Alh Muhd Sani Gadanya
25. 18.Alh Ibrahim Zakari Bagwai
26. Alh Muhammad Inuwa Dabgaɗa
27. Alh Lawan Safiyanu Gogori
28. Alh Sunusi Nassarawa
29. Alh Jibirin Harbau
30. Alh Hamza Tsanyawa
31. Alh Nura ‘Yanchibi
32. Alh Farouk ‘Yanganau
33. Alh Inusa Yusha’u Tsanyawa
34. Gwani Abdullahi Dangwani
35. Comrd Aminu Abdurrahman
36. Eng Bello Gambo Bichi
37. Barr Imam Ghazali Umar
38. Alh Aminu Abdulhamid
39. Alh Bello Gambo Gogori
Ribadu ya fusata kan zarginsa a Kano
Kun ji cewa, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan jihar Kano a kotu kan kalamansa.
Ribadu ya dauki matakin ne kan zarginsa da aka yi da hannu a ruruta rikicin jihar Kano wanda Abdulsalam Aminu Gwarzo ya yi.
Asali: Legit.ng