Ana Cikin Ɗimuwa Bayan Jirgi Daga Kaduna Zuwa Abuja Ya Carke a Daji, Sojoji Sun Ja Daga
Fasinjoji sun shiga fargaba bayan jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja ya samu matsala a tsakiyar daji a Jere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - An shiga ɗimuwa yayin da jirgin kasa makare da fasinjoji ya kauce hanya a cikin daji ana tsaka da tafiya a jihar Kaduna.
Jirgin da ya dauko fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja ya carke ne a Jere da ke kan hanyar Abuja da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Mayu.
Jirgin kasa ya baro Kaduna zuwa Abuja
Jirgin ya baro Kaduna ne da misalin karfe 8:05 na safe zuwa Abuja amma ya samu matsala bayan awa daya da fara tafiya, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An girke jami'an tsaro domin gudun abin da ka iya faruwa a cikin dajin musamman harin yan bindiga.
Leadership ta tabbatar cewa a yanzu haka ana kan gyara inda kusan tarago uku ne suka kauce hanya a jikin jirgin yayin da ake tafiya.
Duk da jirgin ya tsaya ne a yanki mai duwatsu, jami'an sojoji da yan sanda sun hallara domin ba da kariya.
Kaduna: Babu wata sanarwa daga hukumar NRC
Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC) kan lamarin da ya faru a yankin Jere da ke jihar Kaduna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa injiniyoyi suna kan gyara domin daidaita komai yayin da mutane suke cikin dar-dar kan abin ka iya faruwa a wurin.
Fasinjoji sun shiga fargaban ne ganin yadda jirgin ya ɓaci a tsakanin duwatsu inda suke tunanin komai zai iya faruwa.
Jirgin sama ya kauce hanya a Lagos
A wani labarin, kin ji cewa wani jirgin sama dauke da fasinjoji 52 ya gamu da tsautsayi bayan ya kauce hanya a jihar Lagos.
Jirgin, mallakin Xejet Airlines ya kauce hanya ne tare da fantsama cikin daji a cikin filin jirgin saman Lagos.
Jami'an Hukumar kula da jiragen saman ta FAAN sun yi gaggawar kai dauki wurin domin ceto fasinjoji daga halin da suke cikin.
Asali: Legit.ng