Kano: Ribadu Ya Ɗauki Zafi Inda Ya Yi Barazana Ga Aminu Gwarzo, Ya Gindaya Sharuda
- Mallam Nuhu Ribadu ya yi martani mai zafi kan zarginsa da gwamnatin jihar Kano ta yi kan rikicin sarautar jihar
- Ribadu ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan jihar, Abdussalam Aminu Gwarzo a kotu kan kalaman batanci da ya yi a kansa da zarge-zarge
- Hakan ya biyo bayan zargin Ribadu da hannu a kokarin dawo da Aminu Ado karfi da yaji kan karagar mulkin Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka gwamnatin Kano a kotu.
Ribadu ya yi barazanar bayan zarginsa da mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi kan dawo da Aminu Ado Bayero garin Kano.
Zargin Ribadu kan rikicin sarautar Kano
Hakan ya biyo bayan martanin Abdussalam Gwarzo inda ya kira sunan Ribadu a matsayin wanda ya ba Aminu Ado jirage biyu zuwa Kano domin mayar da shi karagar mulki, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata takarda, lauyoyin Ribadu sun bukaci neman afuwa daga mataimakin gwamnan jihar kan wadannan kalamai da ya yi na ɓatanci.
Ribadu zai dauki mummunan mataki kan Gwarzo
"Mun gano wani faifan bidiyo da ke yawo inda mataimakin gwamnan Kano ke zargin Nuhu Ribadu ƙarara a fadar mai martaba sarkin Kano a ranar Asabar 25 ga watan Mayu."
"Kana zargin Ribadu da neman kisan mutanen Kano da kuma lalata dukiyoyinsu a cikin harshen Hausa."
"Dukkan wannan zarge-zarge karya ne kuma nema kake ka batawa Ribadu suna da ofishinsa duk da darajar da ya ke da shi a cikin al'umma."
"Ribadu ya dauki wannan zargi da muhimmanci kuma ya bukaci abubawa biyu daga gare ka cikin awanni 24:
i. Ka janye kalamanka kamar yadda ka yi a gaban mutane da kafofin sadarwa."
ii. Ka nemi afuwa a gidajen jaridu guda biyar da kuma sananniyar kafar gidan jarida ta yanar gizo, sabanin haka Ribadu zai iya daukar matakin shari'a."
- Lauyoyin Ribadu
Ribadu ya musanta hannu a rikicin Kano
Kun ji cewa Mallam Nuhu Ribadu ya musanta hannu a zarginsa da ake yi kan rikicin sarautar jihar Kano.
Ribadu ya ce abin da ake yadawa an yi ne domin bata masa suna kawai a cikin al'umma da kuma jihar Kano.
Asali: Legit.ng