Gwamna Abba Ya Sanya Labule da Sanusi II, Shugabannin Tsaro a Kano, Bayanai Sun Fito

Gwamna Abba Ya Sanya Labule da Sanusi II, Shugabannin Tsaro a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Shugabannin tsaro a Kano sun shiga ganawar sirri da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan dambarwar sarautar jihar
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe rawanin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sannan ya sake naɗa Muhammad Sanusi II bayan ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano
  • Ganawar gwamnan da shugabannin tsaron na zuwa ne bayan sun yi irin wannan ganawar da korarren Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi ll a yanzu haka suna ganawa da shugabannin tsaro a jihar.

Gwamnan da shugabannin tsaron na ganawa ne tare da Sarkin na Kano a fadarsa da ke birnin Kano.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun caɓe, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Kano

Gwamna Abba ya shiga ganawa da shugabannin tsaro
Gwamna Abba ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadar Sarkin Kano Hoto: @KyusufAbba
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun cece-kuce a tsakanin gidan sarautar, lamarin da ya haifar da tashin hankali a faɗin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto kan ganawar gwamnan da shugabannin tsaro a jihar a fadar Sarkin Kano.

Gwamna Abba ya sauke Aminu Ado Bayero

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, Sannan ya naɗa Muhammadu Sanusi II bayan ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano.

Bayan rattaɓa kan dokar Gwamna Abba ya umarci sarakuna guda biyar da sabuwar dokar ta kora da su tattara kayansu su fice daga fada cikin sa'o'i 48.

Yayin da sauran sarakunan guda huɗu suka bi wannan umarnin, Aminu Ado Bayero ya dawo birnin Kano inda ya koma gidan Sarki da ke Nasarawa.

Kara karanta wannan

Manyan jami'an tsaro sun yi watsi da Gwamna, sun isa ƙaramar fadar sarkin Kano

Hakan da tsohon Sarkin ya yi ya sanya gwamnan ya ba jami'an tsaro umarnin cafke shi bisa zarginsa da kawo rikici a jihar.

Bayanai kan ganawar gwamnan da shugabannin tsaron ba su fito ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Jami'an tsaro a fadar gwamnatin Kano

A wani labarin kuma kun ji cewa, an tsaurara matakan tsaro a gidan gwamnati Kano a lokacin da taƙaddama kan sarauta ke ƙara rincaɓewa.

Jami'an tsaro sun mamaye muhimman wurare a gidan gwamnatin duk da ba su hana shige da fice a gidan gwamnatin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel