Ribadu Yana Kokarin Dawo da Aminu Ado Karfi da Yaji Kan Karaga? An Gano Gaskiya

Ribadu Yana Kokarin Dawo da Aminu Ado Karfi da Yaji Kan Karaga? An Gano Gaskiya

  • Yayin da ake zargin Nuhu Ribadu da daukar nauyin dawo da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, an gano gaskiya kan lamarin
  • Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara a bangaren tsaro, Nuhu Rubadu ya karyata cewa yana da hannu game da dawo da Aminu Ado Kano
  • Wannan ya biyo bayan zargin da mataimakin gwamnan Kano, Abdulsalam Aminu ya yi kan Ribadu game da dawo da tsohon Sarki jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano.

Ribadu ya musanta hannu a cikin zargin da ake yi kansa cewa yana kokarin dawo da Aminu Ado Bayero kan karaga a Kano.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya fi ƙarfin doka," Sarkin Kano da aka tsige ya mayar da martani mai zafi

Ribadu ya yi martani kan zargin hannu a rikicin sarautar Kano
Nuhu Ribadu ya musanta hannu a dawo da Aminu Ado Bayero Kano. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

Ribadu ya musanta dawo da Aminu Ado

Mai magana da yawun Ribadu, Zakari Mijinyawa ya shaidawa Premium Times cewa zargin da ake yi ba gaskiya ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mijinyawa ya ce wannan an shirya ne domin cimma wata manufa da wadanda suka kirkiri hakan ke shirin yi, Punch ta tattaro.

Ya ce babu kamshin gaskiya kan cewa Ribadu ya ba da jirage guda biyu domin dawo da Aminu Ado Kano a kokarin mayar da shi karaga.

Ya gargadi ƴan siyasa da su guji furta irin wadannan kalamai da zasu kawo karin matsalar da ake ciki na neman zaman lafiya.

Aminu Ado: Zargin gwamnatin Kano kan Ribadu

Wannan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdulsalam Aminu ya zargi Ribadu da daukar nauyin dawo da Aminu Ado.

Aminu ya ce Ribadu ya dauki nauyin jirage guda biyu domin dauko Aminu Ado zuwa Kano yayin da aka tube shi a sarautar jihar.

Kara karanta wannan

'Muna shirin raka sarki ado bayero fadarsa a kofar kudu,' Tsohon Kwamshina

Malamai sun tsoma baki a matsalar Kano

Kun ji cewa Majalisar malaman jihar Kano ta yi martani kan abin da ke faruwa a jihar kan matsalar sarautar da ke faruwa.

Malaman sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar ba tare ta jawo tashin hankali ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Malaman Musuluncin suka fitar a yau Asabar 25 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.