Manyan Jami'an Tsaro Sun Yi Watsi da Gwamna, Sun Isa Ƙaramar Fadar Sarkin Kano

Manyan Jami'an Tsaro Sun Yi Watsi da Gwamna, Sun Isa Ƙaramar Fadar Sarkin Kano

  • Shugabannin tsaro a jihar Kano sun isa ƙaramar fadar Sarki ta Ƙofar Kudd, inda tsohon sarki Aminu Ado Bayero ke ciki
  • Wannan na zuwa ne mintoci kaɗan bayan hukumomin tsaron jihar sun ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba na kama tsohon sarkin Abba
  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya koma fadar Ƙofar Kudu da sanyin safiyar yau Asabar, 25 ga watan Mayu, 2024 tare da rakiyar gwamna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Manyan jami'an tsaro a jihar Kano sun isa cikin ƙaramar fada da ke Kofar Kudd inda tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki yanzu haka.

Kwamishinan ƴan sanda, CP Usaini Gumel, kwamandan sojoji, MA Sadiq, kwamandan hukumar tsaron fararen hula NSCC ML Falala na cikin waɗanda suka gana da Aminu Ado.

Kara karanta wannan

'Muna shirin raka sarki ado bayero fadarsa a kofar kudu,' Tsohon Kwamshina

Aminu Ado Bayero.
Darktan DSS da wasu manyan jami'an tsaro a Kano sun ziyarci Aminu Ado a fadar Kofar Kudd Hoto: @KabiruMisali
Asali: Twitter

Wannan na zuwa yayin da lamurra ke ƙara dagulewa game da karagar sarkin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi ya shiga fadar Kofar Kudu

Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, wanda ya koma cikin fadar Ƙofar Kudu da sanyin safiyar ranar Asabar ɗin da muke ciki.

A rahoton jaridar Daily Trust, Sarki Aminu Ado Bayero, wanda Gwamna Abba ya tsige ya dawo cikin birnin Kano a daren jiya Alhamis.

Tsigaggen Sarkin ya koma ƙaramar fadar Ƙofar Kudd tare da tsattsauran matakan tsaron da ke tare da shi.

Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a kamo Aminu Ado Bayero bisa zargin yunƙurin ta da tarzoma da kuma ruguza tsaron jihar Kano.

Jami'an tsaro suna saɓa umarnin Abba

Jim kaɗan bayan haka ne jami'an tsaron suka bayyana cewa ba zamu kama tsohon sarkin ba kamar yadda gwamna ya umarta, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun caɓe, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Kano

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Mohammed Usain Gumel, ne ya sanar da haka a madadin hukumomin tsaro yayin hira wa manema labarai a hedkwatar ƴan sanda.

Matasa sun cika fadar sarkin Kano

A wani rahoton kuma Abubuwa sun fara rincabewa yayin da aka fara zaman dar-dar a Kano bayan matasa sun cika harabar fardar Sarkin Kano da makamai.

Mafi yawan matasan sun haɗa da masu goyon bayan tsohon Sarki, Aminu Ado Bayero da kuma Muhammad Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262