Mataimakin Gwamna Ya Bayyana Wanda ake Zargi da Kitsa Rikicin Masarautar Kano

Mataimakin Gwamna Ya Bayyana Wanda ake Zargi da Kitsa Rikicin Masarautar Kano

  • Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi magana kan rikicin da ke ƙoƙarin ɓarkewa kan masarautar Kano bayan dawowar tsohon sarki Aminu Ado Bayero
  • Aminu Abdulsalam Gwarzo ya zargi mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da taimakawa tuɓaɓɓen sarkin na Kano
  • Mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu ya samar da jirage guda biyu domin dawo da Aminu Ado Bayero zuwa Kano tare da kai shi zuwa fada

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da hannu kan rikicin sarautar Kano.

Mataimakin gwamnan ya zargi Nuhu Ribadu da kitsa yadda za a dawo da Aminu Ado Bayero a fada.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ya koma fada a Kano, bidiyo ya fito

Masarautar Kano ta fada cikin rikici
Mataimakin gwamnan Kano ya zargi Nuhu Ribadu da hannu a rikicin masarauta Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Matasan Faidha
Asali: Facebook

Wane zargi mataimakin gwamnan Kano ya yi?

Aminu Abdulsalam a wata ƴar gajeriyar hira ta faifan bidiyo a fadar sarki da ke Gidan Rumfa a ranar Asabar, ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu ya ba da jirage guda biyu domin kawo Aminu Ado Bayero Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya ba da jiragen sama guda biyu domin kawo tuɓaɓɓen sarki zuwa Kano sannan da kai shi zuwa fada. Ba mu fahimci manufarsu ba."

- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Aminu Ado Bayero, wanda ya kai ziyara ga Awujale na Ijebuland a jihar Ogun, jama’a sun tarbe shi a Kano da sanyin safiyar Asabar, inda ya koma wata ƙaramar fada da ke Nassarawa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ya ba da umarnin a cafke tsohon sarkin bisa zarginsa da kawo rikici a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

Aminu Ado Bayero ya isa fada

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma birnin Kano kwanaki bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe masa rawanin sarauta.

Tsohon sarkin ya yi masauki a tsohon gidan Sarki da ke Nasarawa a cikin birnin Kano yayin da ɗimbin magoya bayansa suka fito domin yi masa maraba.

Dawowarsa na zuwa ne bayan Gwamna ya naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano tare da rusa sauran masarautun da aka ƙirƙiro a lokacin mulkin Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel