Gwamna Radda Ya Kawo Hanyar Magance Rashin Tsaro a Najeriya

Gwamna Radda Ya Kawo Hanyar Magance Rashin Tsaro a Najeriya

  • Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar nan shekara da shekaru
  • Gwamnan ya buƙaci gwamnati da ta karɓe ikon wuraren da ba su a ƙarƙashin ikonta domin kawo ƙarshen matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa
  • Ya kuma buƙaci gwamnati ta kula da tsaron iyakokin ƙasar nan tare da yaƙi da cin hanci da rashawa waɗanda duk suna taimakawa wajen taɓarɓarewar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi magana kan hanyar magance matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Gwamnan ya jaddada buƙatar gwamnati ta mamaye tare da rage wuraren da ba su ƙarƙashin ikonta.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: DHQ ta kalubalanci gwamna kan zargin sojoji na hada baki da 'yan bindiga

Dikko Radda ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamna Dikko Radda ya tabo batun matsalar rashin tsaro a Najeriya Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Ya kuma nuna buƙatar magance matsalar iyakokin ƙasar nan tare da kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, inda ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lacca a jami’ar tarayya da ke Gusau, cewar rahoton tashar Channels tv.

Me Radda ya ce kan rashin tsaro?

Ya bayyana jahilci, wariya, rashin shugabanci mai kyau, rashin mutunta addinin juna da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a matsayin manyan abubuwan da ke kawo tabarbarewar tsaro wanda ke kawo illa ga ci gaban ilimi.

Gwamna Radda ya ce, yawaitar sace yara ƴan makaranta raba mutane da matsugunansu na haifar da ɗimbin yaran da ba su isa zuwa makaranta wanda hakan koma baya ne a ƙasar nan.

Ya yi kira ga masu kula da makarantu da su gina katanga a makarantun domin hana sace mutane, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya wanke Tinubu daga zargin wuyar da ake sha a Najeriya

Gwamnan ya bayyana cewa yara ƴan makaranta a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara a yankin Arewa maso Yamma na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga da sace-sace domin neman kuɗin fansa.

Dakile ƴan bindiga a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatinsa ta samu galaba kan ta'addanci da ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa aƙalla ya dakile matsalar tsaron jihar da kaso 70% cikin kaso 100% a shekara ɗaya da ya yi a kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng