An Yankewa Masu Kwacen Waya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya a Jihar Ekiti

An Yankewa Masu Kwacen Waya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya a Jihar Ekiti

  • Wata kotu a jihar Ekiti ta yankewa masu fashi da makami da satar waya hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Alkallin kotun mai shari'a Blessing Ajireye ta ce an yanke musu hukuncin ne bayan an kama su da laifi dumu dumi
  • Har ila yau kotun ta bayyana irin makaman da aka kama barayin da su da kuma irin laifuffukan da suka aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti - An gurfanar da wasu barayin waya da na'urar cajin waya su biyu a gaban wata kotu a jihar Ekiti.

Kotun
Za a rataye masu kwacen waya a Ekiti. Hoto: Hoto: Witthaya Prasongsin
Asali: Getty Images

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa bayan zaman kotun an yankewa mutanen hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta ji wuta, ta ba da tulin kyaututtuka ga ƴan mata 100 da za a aurar

Alkalin kotun ta tabbatar da cewa an yanke musu hukuncin ne bayan an kama su da laifi dumi-dumu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka gurfanar da barayin wayar?

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gurfanar da mutanen ne gaban kotu tun watan Disambar shekarar 2022.

A zaman kotun, mai Shari'a Blessing Ajireye ta bayyana cewa barayin sun aikata satar ne a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 2022.

Laifin da barayin wayar suka aikata

Kotun ta bayyana cewa an kama barayin da laifin fashi da makami da mallakar makamai masu muni, rahoton Peoples Gazette.

Cikin makaman da aka kama barayin da su akwai bindigogi, wukake da adduna wanda da su suke amfani wajen aikata ayyukan ta'addanci.

Abubuwan da barayin suka sace

Cikin ayyukan sata da suke gudanarwa da kayan da suka tara an same su da wayoyi da suka yiwa masu mutane fashi.

Kara karanta wannan

An kama dan sandan bogi dauke da takardun kotun karya a Legas

Har ila yau an same su da na'urar cajin waya da katin cire kudi a banki da kudi N105,000 da suka sace a wajen wasu mutane.

Bayan shaidu sun ba da shaida kan mutanen sai mai shari'a Blessing Ajireye ta yanke musu hukuncin daurin kisa ta hanyar rataya.

Uba ya kai dansa kara kotu

A wani rahoton, kun ji cewa wani mahaifi da ya nemi a boye sunansa ya shigar da dan cikinsa kara kotun shari'ar Muslunci da ke Fagge a jihar Kano.

A zaman kotun, mai gabatar da kara Malam Abdul Wada ya bayyanawa wanda ake zargi laifuffukansa kuma ya amince, daga baya alkali ya dauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel