Jami'in Dan Sanda Ya Harbe Farar Hula Har Lahira a Abuja

Jami'in Dan Sanda Ya Harbe Farar Hula Har Lahira a Abuja

  • Wani dan sanda a birnin tarayya Abuja ya harbe farar hula har lahira bayan sun yi jayayya kan tafiya caji ofis
  • Lamarin ya faru ne bayan marigayin mai suna Onyebuchi Anene ya yi hatsari da wani mai acaba a yankin Kubwa
  • Rundunar yan sandan birnin tarayya ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana matakin da ta dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A ranar Laraba ne wani jami'in dan sanda ya harbe wani mutum har lahira a birnin tarayya Abuja.

Police
Dan sanda ya harbe wani mutum bayan sun yi jayayya a Abuja. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dan sandan ya harbe mutumin mai suna Onyebuchi Anene a lokacin da suke jayayya.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure da aka bindige ɗan sanda a tsakiyar kasuwar Jos

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa rikicin ya fara ne bayan Onyebuchi Anene ya yi ƙaramin hadari da mai acaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan sanda ya harbe Onyebuchi

Bayan Onyebuchi ya samu hadari da dan acaba, sun yi kokari sun sasanta a tsakaninsu cikin kankanin lokaci.

Suna ƙoƙarin tafiya sai ga dan sandan ya zo wurin da suka yi hatsarin yana neman mayar da matsalar sabuwa fil.

Dan sandan ya bukaci Onyebuchi da mai acaba su tafi caji ofis amma suka nuna gardama a kan hakan.

Sun bayyanawa dan sandan cewa sun riga sun sasanta amma duk da haka yace sai an je caji ofis.

Ana haka ne sai dan sandan ya harbi Onyebuchi, nan take aka tafi asibiti da shi amma ana zuwa rai ya yi halinsa.

Yan sanda sun tabbatar da harbin

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fadi ainihin lokacin da ya fara mulkin jihar Rivers

Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja SP Adehb Josephine ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa kwamishinan yan sanda ya ce a gaggauta bincike kan lamarin.

Ta kara da cewa an harbi Onyebuchi Anene ne a ranar Laraba da misalin karfe 4:45 na yamma a Byazhin da ke Kubwa, rahotom Daily Post.

An kama yan sanda a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu daga cikin jami'anta da ake zargi da yin garkuwa da wani dan kasuwa a Abuja.

Dan takarar jam'iyyar LP a zaben 2023, Harrison Gwamnishu ya fara fitar da labarin yin garkuwa da dan kasuwar kafin daga baya rundunar ta dauki mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel