Sarki Sanusi II Ya Dawo Gida, Ya Isa Fadar Gwamnatin Kano a Shirin Komawa Sarauta
- Rahotanni sun nuna cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa gidan gwamnatin jihar Kano da safiyar ranar Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024
- Sarkin zai karɓi takadar mayar da shi kan kujerar sarautar Kano daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf sannan ya wuce fadar Nasarawa
- Ana sa ran Sarki Sanusi zai halarci taron hawan doki a gidan gwamnati kuma zai jagoranci sallar Jumu'a a babban masallaci da ke fadar Ƙofar Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya isa fadar gwamnatin jihar domin karɓar takardar shaidar dawowarsa kan karagar sarauta.
A yau Jumu'a, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai miƙa wa Sarki Sanusi II takardar shaidar mayar da shi kan kujerar sarauta ɗaya tilo mai daraja a jihar Kano.
An tattaro cewa Sarkin ya koma Kano da yammacin ranar Alhamis kuma an shirya masa ƙaramar liyafar maraba da zuwa gida saboda shawarwarin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, zuwa yanzu an kammala duk wasu shirye-shirye na sake fitowar Sanusi II a matsayin Sarki karon farko bayan mayar da shi a sarauta.
Ana sa ran Sarki Sanusi zai je ɗakin taron Africa House da ke cikin gidan gwamnatin Kano domin halartar hawan dawaki na murnar dawowarsa da misalin ƙarfe 10:00 na safe
Sarki Sanusi zai shiga fada yau
Daga nan kuma zai wuce fadar mai martaba Sarkin Kano da ke Nasarawa a cikin ƙwaryar birni.
Bayan haka ne Mai Martaba Sarki Sanusi zai wuce zuwa babban masallacin Kano da ke fadar Ƙofar Kudu domin jagorantar sallar Jumu'a yau 24 ga watan Mayu, 2024.
A ranar Alhamis ne Gwamna Abba Yusuf ya sake nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano, shekaru hudu bayan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya tsige shi.
Bugu da kari, gwamnan ya sauke sarakuna biyar da Ganduje ya nada tare da ba su wa'adin sa'o'i 48 da su bar masarautunsu, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Abubuwa 7 game da Sanusi
Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Sarkin Kano na 14 a tarihi, Muhammadu Sanusi na II.
Idan za ku iya tunawa a 2020, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sarki Sanusi II kuma ya maye gurbinsa da Alhaji Aminu Ado Bayero.
Asali: Legit.ng