Sheikh Bala Lau Ya Kai 'Dan Agajin Izala da Ya Dawo da Kudin Tsintuwa Hajji

Sheikh Bala Lau Ya Kai 'Dan Agajin Izala da Ya Dawo da Kudin Tsintuwa Hajji

  • Kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta cika alkawarin kai dan agaji hajji
  • A watan Maris da ya wuce ne kungiyar ta karrama dan agajin da kyaututtuka masu gwabi sannan ta masa alkawarin kujerar hajji
  • Legit ta tattauna da dan agaji, Ibrahim Abdullahi kan yadda suka ji da irin karramawar da abokin aikinsu ya samu da kuma yadda hakan zai karfafe su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta cika alkawarin kai dan agaji aikin hajji.

Izala
Izala ta kai dan agaji hajji saboda halin gaskiya. Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Gaskiya ta kawowa 'dan agaji kujerar hajji

A jiya Alhamis ne dan agajin mai suna Salihu Abdulhadi ya samu tafiya Saudiyya domin aikin hajji kamar yadda kungiyar ta sanar a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Hanyoyin samun kudi sun yi karanci bayan tafiyar El-Rufai, an samo mafita a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hotunan da kungiyar ta wallafa an hango dan agajin, Sheikh Abdullahi Bala Lau da sauran malamai suna bankwana, zai je sauke farali.

Dalilin kai dan agajin aikin hajji

Dan agajin ya samu karramawar ne saboda gaskiya da ya nuna a lokacin da ya tsinci makudan kudi.

Salihu ya tsinci kudi sama da N100m na wata mata kuma ya mayar mata ba tare da tantama ba, kamar yadda sheikh Bala Lau ya bayyana.

Yaushe aka masa alkawarin hajji?

Duk da cewa ba a samu bayanai kan lokacin da ya tsinci kudin ba, amma kungiyar Izala ta yiwa Salihu alƙawarin hajji ne a watan Maris da ya wuce.

Hakan ya faru ne a lokacin rufe taron karawa juna sani da kungiyar ta shirya ga malamai masu tafsirin Ramadan a jihar Bauchi.

Kyautattukan da dan agajin ya samu

Kara karanta wannan

Tinubu zai kaddamar da jirgin kasan Abuja, ya yi albishir 1 ga yan Najeriya

A lokacin da aka karrama Salihu Abdulhadi, ya samu kyautattuka da dama daga manyan mutane a fadin Najeriya.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ba shi kyautar mota, Abdulmalik Zannan Bandugu ya ba shi kyautar N2m.

Legit ta tattauna da dan agaji

Wani dan agaji, Ibrahim Abdullahi ya nuna farinciki kan yadda aka karamma abokin aikinsu sannan ya kara da cewa hakan ya kara bayyanawa duniya waye dan agaji.

Dan agajin ya kuma tabbatarwa Legit cewa a yanzu haka mutane da dama suna yabon aikin agaji ciki har da wadanda ba Musulmai ba.

Izala ta fara alkunut Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta sanar da fara al-kunut kan halin kuncin da Najeriya ke ciki.

Shugaban kungiyar na jihar Gombe, Salisu Muhammad Gombe ne ya bayar da sanarwar yayin wani taro da suka gudanar kan tafsirin azumin da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel