Kano: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Sabuwar Dokar Rusa Masarautu
Majalisar dokokin Kano ta rusa masarautun jihar guda biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Hakan ya tabbatar da cewa dukkan sarakuna biyar na masarautun sun rasa kujerunsu.
Abubuwan da ke cikin dokar masarautar Kano
Hakan bai rasa nasaba da takun-saka tsakanin gwamnatin Abba Kabir da tsohuwar gwamnatin da ta shude, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku wasu muhimman abubuwa kan sabuwar dokar a Kano.
1. Lalata dokar da aka dabbaka a 2019
Sabuwar dokar da majalisar ta kawo ta rusa tsohuwar dokar kafa masarautun biyar da gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2019 da dukkan abubuwa da ke kunshe cikinta.
Hakan ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da ke kunshe cikin dokar babu su a yanzu.
2. Rusa dukkan sababbin masarautun Kano
Dokar ta rusa masaraurun da aka kirkira a 2019 da ya haɗa da dukkan mukamai da kuma wasu hagalare a cikin dokar.
Dukkan mutane da suka karin girma a cikin dokar an rusa su an dawo sabuwar doka kafin 2019 da ta gabata.
3. Dawo da mukamai da sarautun gargajiya
Mutanen da suka samu mukamai da sarauta zasu dawo matsayinsu na da idan har akwai gurbinsu a sabuwar dokar.
An dauki wannan mataki ne domin dawo da martabar masarautun jihar da ke cike da tarihi.
4. Karfin ikon Abba Kabir a Kano
Gwamna Abba Kabir ya na da ikon daukar dukkan matakai domin dawo da dokar baya game da masaraurun.
Wannan ya haɗa da dawo da wasu mukamai ko gyararraki dangane da dokar kafin sauyata a 2019.
5. Aikin Kwamishinan ƙananan hukumomi
Kwamishinan kananan hukumomi a jihar shi ke da alhakin kula da dukkan sauya sarautun da aka rusa.
Zai kula da mika kadarori da duk wasu abubuwa da suka shafi tsofaffin masarautun.
Majalisa ta rusa masarautun Kano
Kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rusa dukkan masarautu biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Majalisar ta dauki matakin ne da safiyar yau Alhamis 23 ga watan Mayu bayan dokar ta tsallake karatu na uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng