'Mun Zabi Gwamna, ya Saka Mana da Rashin Adalci," Wakili a Masarautar Gaya

'Mun Zabi Gwamna, ya Saka Mana da Rashin Adalci," Wakili a Masarautar Gaya

  • Al'umma a jihar Kano na bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan rushe dukkanin masarautun Kano guda biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta nada
  • Wasu a masarautar Gaya sun yi kakkausar suka ga Abba Kabir Yusuf da 'yan majalisar dokokin jihar, inda suka ce tsige sarakunan rashin adalci ne karara
  • Wakili a masarautar Gaya, Faruq Tajo ya shaidawa Legit Hausa cewa sun zabi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ne domin kawo musu mafita ba tsige sarakuna ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Masarautar Gaya daya ce daga masarautun Kano biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kafa, bayan tsige Sarki Muhammadu Sunusi II.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga mayar da Sanusi II gidan sarauta

Wasu daga cikin wakilan masarautar na ganin gwamnatin Kano ba ta yi musu adalci ba da ta rushe masarautun a yau.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Kano ta amince da kudurin da ya rushe dukkanin masarautun Kano biyar, inda shugaban masu rinjaye, Lawal Dala ya ce babu sarki a Kano.

Abba Kabir Yusuf
Mazauna Kano sun magantu kan tsige sarakunan kano biyar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba ta fito karara ta sanar da masu sauraro mataki na gaba ba, amma rahotanni na bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta nada Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon sarki kamar yadda Leadership News ta Wallafa.

Kano: Me wakilan masarauta ke cewa?

Al'ummar Kano da suka jibanci masarauta na ci gaba da tofa albarkin bakinsu kan tsige sarakunan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf tayi a yau.

Wakilin masarautar Gaya a bangaren gine-gine, Faruq Tajo ya bayyana cewa gwamnati ba ta yi musu adalci ba, domin sun zabe ta.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Gwamna Abba ya mayar da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano

"Abin da wannan gwamnati ta yi mana, ba ta yi dai-dai ba, ba ta yi mana adalci ba domin mun zabe ta.
Kuma mu ba mu zabe ta domin haka ba, domin ci gaba ne kuma mun yi mata fatan alheri domin mun yi mata kyakkyawan zato."

- Faruq Tajo

Wakili a rushashshiyar masarautar Gaya ya nanata cewa ba su zabi gwamnatin da 'yan majalisun domin cire sarakuna ba, sai dai samar musu ayyukan more rayuwa.

DSS sun mamaye fadar sarkin Kano

A baya mun kawo muku labarin cewa jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta mamaye fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero jim kadan bayan gwamnati ta tsige shi daga sarautar Kano.

Ana rade-radin cewa zuwa anjima kadan gwamna Abba Kabir Yusuf zai rattaba hannu kan dokar sannan za a nada sabon sarki nan ba da jimawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.