Jami'an Hukumar DSS Sun Mamaye Fadar Mai Martaba Sarkin Kano

Jami'an Hukumar DSS Sun Mamaye Fadar Mai Martaba Sarkin Kano

  • Yayin da rahoton rushe masaurautun Kano ya bazu, jami'an DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero
  • Jami'an tsaron sun tare kofar shiga fadar sarkin da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Alhamis, 23 ga watan Mayu, 2023
  • Ana ƙishin-ƙishin cewa idan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a sabuwar dokar da yiwuwar gwamnatinsa za ta canza Sarkin Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jami'an hukumar tsaron farin kaya watau DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da safiyar yau Alhamis.

Wannan na zuwa ne yayin rahotanni suka bazu cewa majalisar dokokin jihar ta tsige Sarki Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya naɗa.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Bayan sauya dokar masarautu, jam'an DSS sun mamaye fadar sarkin Kano Hoto: @KabiruMisali
Asali: Twitter

A ɗazu ne majalisar dokokin ta amince da kudirin yi wa dokar masarautu garambawul, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an DSS sun dira fadar Sarkin Kano

Yayin da wakilin Daily Trust ya ziyarci fadar Sarkin Kano da misalin karfe 11:00, ya taras an girke dakarun hukumar DSS a fadar Sarkin.

Duk da Sarki Aminu Ado Bayero baya nan, an ga jami'an tsaro sun mamaye ƙofar shiga fadar sarkin suna jiran abin da ka iya zuwa komo.

Ina Sarki Aminu Ado Bayero?

Legit Hausa ta fahimci cewa Sarki Aminu Ado Bayero yana jihar Ogun a wata ziyara ya da kai wa Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona.

Gyaran da majalisa ta yi wa dokar masarautun ya sauke dukkan sarakunan da tsohon gwamna Ganduje ya kirƙiro lokacin mulkinsa.

Gwamna Abba zai naɗa sabon Sarki

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

Kuma ana raɗe-raɗin cewa idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu a kan dokar, da yiwuwar za a tsige Aminu Ado Bayero, rahoton The Nation.

Kudirin da majalisar dokokin ta amince da shi ya bai wa mai girma gwamna damar ɗaukar dukkan matakan da ya dace domim dawo a martabar masarautar Kano.

Majalisa ta tsige Aminu Ado Bayero?

Wani rahoton kun ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Kano ya ce kudirin dokar da suka yi ya soke dukkan sarakunan da aka naɗa a 2019.

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na cikin waɗanda wannan matakin ya shafa tare da sauran sarakuna huɗu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel