Notcoin vs TapSwap: Abubuwa 5 Game da Tara Kudin Crypto Ta Hanyar Dangwale a Telegram

Notcoin vs TapSwap: Abubuwa 5 Game da Tara Kudin Crypto Ta Hanyar Dangwale a Telegram

  • Biyo bayan samun makudan kudi sanadiyyar fashewar Notcoin, mutane da dama sun fada harkar kirifto ba dare ba rana
  • A wuraren ibada, makarantu, wuraren zama da gidaje, yara da manya kowa ya shiga harkar dangwale domin neman kudin kirifto
  • Legit ta tattauna da wani dan Crypto, Aminu Muhammad Baba kan yadda suke tsammanin samun daloli idan Tapwsap ya fashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A 'yan kwanakin nan, harkokin neman kudi ta hanyar kirifto ya mamaye kafafen sadarwa.

Kirifto
An bayyana abubuwa masu muhimmanci a kan Notcoin da Tapswap. Hoto: @iam_safee, Bitcoin News, Nairametrics
Asali: TikTok

Yawanci tattaunawar da ake yi ta fi mayar da hankali kan Notcoin da ta fashe ko kuma Tapswap da ke kokarin fashewa.

A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku bayanai masu muhimmanci kan yadda za ku samu fa'ida a harkar dangwalen Tapswap da ma karin ilimin Notcoin.

Kara karanta wannan

Tapswap ya fadi dalilin matsalar da ƴan Najeriya ke fuskanta a dangwale, ya ba da haƙuri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ma'anar Notcoin da Tapswap

A jawabin da Binance suka yi, sun nuna cewa Notcoin wani kudi ne na yanar gizo wanda ake samu ta hanyar amfani da manhajar Telegram.

Hakazalika, Tapswap shi ma wata harka ce da ake samun kuɗi ta manhajar Telegram kamar yadda kamfanin ya bayyana a shafinsa na X.

2. Har yanzu Tapswap bai fashe ba

Biyo bayan fashewar Notcoin a kwanakin baya, mutane da dama sun shiga harkar dangwalen Tapswap domin samun na kashewa.

Ana sa ran cewa Tapswap zai fashe a ranar 30 ga watan Mayu duk da cewa har yanzu al'umma na cigaba da dangwale a manhajar Telegram domin tara kudi, rahoton Medium Reports.

3. An kulle dangwalen Notcoin

Kamfanin Notcoin ya sanar da kammala dangwale domin tara kudi ta manhajar Telegram tun ranar 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su rika shiga Tapswap a saukake, batun matsalar ya fito

Sai dai har yanzu ana cigaba da dangwalen Tapswap a manhajar ta Telegram domin cigaba da tara kudi.

4. Ba bukatar kwarewa kafin fara Tapswap

Babu bukar kwarewa ta musamman a yayin da mutum zai fara harkar dangwalen domin tare kudi ta manhajar Telegram.

An saukaka dangwalen Notcoin da Tapswap ta yadda kowa zai iya da zarar an nuna masa yadda zai fara.

5. Tapswap zai fi Notcoin albarka?

Wani masanin kirifto da ya tattauna da Legit, Obani Nwokoma ya ce a bisa dukkan alamu Tapswap zai fi Notcoin albarka idan ya fashe.

A cewar Obani Nwokoma, akwai tsare-tsaren da Tapswap ya zo da su wanda babu su a Notcoin, saboda haka masana suke ganin za a sha romo sosai idan Tapswap ya fashe.

Legit ta tattauna da dan Crypto

Wani dan Crypto, Aminu Muhammad Baba ya bayyanawa Legit cewa suna nan ba dare ba rana suna cigaba da dangwale ta mahajar Telegram domin tsammanin samun daloli.

Kara karanta wannan

"Tapswap ya daina aiki": Budurwa ta yi bayani game da mining ɗin da ƴan Najeriya ke yi

Ya ce duk da bai samu kudi a Notcoin ba, kamar yadda hasashe ya bayyana yana tsammanin samun arziki sosai idan Tapswap ya fashe.

Kwastam ta kama kayan kirifto a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa reshen jihar Lagos ta sanar da abubuwan da ta kama daga watan Janairu zuwa Afrilun shekarar 2024.

Kwamandan hukumar na jihar Lagos, Charles Orbih ne ya bayyana haka ga manema labarai kuma ya lissafa kaya da suka kama ciki har da na'urorin kirifto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng