'Yan Majalisar APC Sun Dauki Mataki Yayin Gyara Dokar Masarautun Kano

'Yan Majalisar APC Sun Dauki Mataki Yayin Gyara Dokar Masarautun Kano

  • Ƴan jam'iyyar APC a majalisar dokokin jihar Kano a yayin zamanta na ranar Alhamis sun tattara kayansu sun fice daga zauren majalisar
  • Ƴan majalisar na jam'iyyar adawa a Kano sun fice daga zauren majalisar ne yayin da ake yunƙurin yi wa dokar da ta kafa masarautun jihar garambawul
  • Majalisar dokokin dai za ta yi wa dokar gyara ne wacce aka amince da ita a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mambobin jam'iyyar APC a majalisar dokokin jihar Kano sun ɗauki matakin ficewa daga zauren majalisar a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayun 2024.

Ƴan majalisar na jam'iyyar adawar a jihar Kano sun fice daga majalisar ne yayin zaman majalisar take gudanarwa na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta rusa duka Sarakunan da Gwamnatin Ganduje ta kirkiro a 2019

'Yan majalisar APC sun fice daga majalisa a Kano
'Yan majalisar APC sun fice daga majalisa yayin yi wa dokar da tsige Sanusi II garambawul Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Meyasa ƴan APC suka fice daga majaliasa?

Tashar Freedom Radio ta kawo rahoton cewa ƴan majalisar na jam'iyyar APC sun daga zauren majalisar ne yayin da ake yunƙurin yi wa dokar kafa masarautun jihar garambawul.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yau ne dai majalisar dokokin ta jihar Kano za ta kammala garambawul ɗin da take yi kan dokar kafa masarautun jihar wacce aka amince da ita a lokacin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar zai iya rattaɓa hannu kan ƙuɗirin gyara dokar masarautun da zarar majalisar dokokin ta amince da shi.

An girke jami'an tsaro a majalisar Kano

A ranar Laraba an girke jami'an tsaro a majalisar dokokin jihar Kano yayin da ƴan majalisar za su yi karatu na biyu kan ƙudirin yi wa dokar kafa masarautun garambawul.

Zaman majalisar domin karanta kuɗirin dokar ya samu halartar ƴan majalisun jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano da na jam'iyyar adawa ta APC.

Kara karanta wannan

Saurautar Kano: Yau za a daddale kan yiwa dokar da ta tsige Sanusi II garambawul

Batun rushe masarautun Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin jihar Kano sun so rushe masarautun Kano kwanaki 20 bayan rantsar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a madafun ikon jihar

Ɗaya daga cikin jagororin majalisar ne ya bayyana haka yayin da majalisar ta fara zaman gyara dokar da ta kirkiro masarautu biyar a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel