Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki

Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki

- Masarautar Kano ta musanta hannunta a siyar da filayen Gandun Sarki dake Dorayi karama ta karamar hukumar Gwale

- Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano tana tuhumar masarautar da siyar da filaye masu yawan kadada 22 tare da waskar da kudin

- Masarautar tace babu hannunta kuma bata san komai a kai ba amma ta fara bincike wanda zata mika ga hukumar yaki da rashawan

Masarautar Kano ta musanta siyar da filayen Gandun Sarki wadanda yasa hukumar yaki da rashawa ta jihar kano take tuhumar Sarki Aminu Bayero da shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawan tana bincikar masarautar akan zargin siyar da filaye har kadada 22 dake Gandun Sarki a Dorayi Karama ta karamar hukumae Gwale dake jihar Kano tare da waskar da kudin zuwa aljihunsu.

Takardun karar da wani wanda ya siya filin, Alhaji Yusuf Aliyu ya shigar, ta bukaci kotun da ta dakatar da shugaban hukumar daga hana su aikin ginin da suka fara.

Bayanan sun kara da cewa masaraurtar ta siyar da kadada 14 daga cikin 22 a kan kudi naira miliyan 200 yayin da sauran magadan Ado Bayero suka siyar da sauran kadada 8 a kan naira miliyan 575.

KU KARANTA: Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola

Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki
Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

Amma kuma a martanin da masarautar tayi bayan tuhumarta da PCACC tayi, tace bata taba aminta da siyar da filayen ba.

A wasikar mai kwanan wata 15 ga Afirilu, wacce Alhaji Abba Yusuf, sakataren masarautar yasa hannu, ta ce: "An umarceni da in sanar da cewa masarautar Kano bata bada amincewarta ba wurin siyar da filayen Gandun Sarki dake Dorayi.

"Don haka duk wanda ya siya, ya siya babu. Bata taba siyarwa Ja'en B and Sons ba ko kuma Cityscape Properties Ltd."

Ta cigaba da cewa: "Masarautarta ta damu matuka da zargin da ake wa wasu jama'a wadanda ma'aikata ne a masarautar. Kamar yadda ya dace, masarautar ta fara bincike kan lamarin kuma zata mika abinda ta gano ga hukumar."

Daga bisani, masarautar tana kira ga hukumar yaki da rashawa da tayi hakuri kuma ta jure har zuwa lokacin da zata kammala bincikenta.

A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, a ranar Lahadi, ya dira Maiduguri tare da rakiyar shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor tare da sauran hafsoshin tsaro, domin duba yanayin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a jihar.

A yayin karbar ministan da tawagarsa a hedkwatar Operation Lafiya Dole a Maiduguri, kwamandan rundunar Manjo Janar Farouq Yahaya, ya jinjinawa yadda minstan, shugaban ma'aikatan tsaro da sauran hafsoshin tsaro ke nunawa.

Ya ce dakarun suna godiya ga ministan a kan ziyarar suke kai musu tare da tabbatar da cewa ministan tare da sauran shugabannin tsaron sun ziyarcesu bayan nada su da aka yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel