'Yan Sanda Sun Ceto Mata da Jariri Daga Hannun Yan Bindiga a Kwara

'Yan Sanda Sun Ceto Mata da Jariri Daga Hannun Yan Bindiga a Kwara

  • Yan sanda sun sanar ceto mata da yaro mai shekaru biyu da masu garkuwa da mutane suka kama a jihar Kwara
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da ceto matan tare da bayyana yadda aka kubutar da su daga jeji
  • Shugaban matasan Kwara ta kudu, Olaitan Oyin-Zubair ya mika sako na musamman ga rundunar 'yan sandan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Rundunar yan sanda a jihar kwara ta gudanar da samame bayan sace wasu mata yan kasuwa da masu garkuwa da mutane suka yi.

Police Ig
Yan sanda sun ceto dan jinjiri a hannun yan bindiga. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kakakin rundunar ya bayyana mata nasarar da rundunar ta samu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tunkari Abuja da tsakar rana, sun fafata da yan sanda

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama matan ne a yankin Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar ta Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin 'yan sanda bayan ceto jama'a

Kakakin yan sandar jihar, Toun Ejire-Adeyemi ta bayyana cewa sun kubutar da mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane, rahoton Vanguard.

Toun Ejire-Adeyemi ta kara da cewa cikin mutane 12 da suka ceto 11 mata mata ne sai dayan kuma jariri mai shekaru 2 da haihuwa.

Kakakin ta ce yanzu haka an mika mutanen ga iyalansu, waɗanda suka samu raunuka kuma suna karbar kulawa a asibiti.

Yadda 'yan bindiga suka yi awon-gaba da su

Har ila yau kakakin yan sandar ta bayyana cewa lokacin da aka kama matan suna dawowa da kasuwa ne, daga kamasu kuma sai yan bindigar suka wuce da su jeji.

Lokacin da labari ya isa wajen yan sanda sun fantsama cikin jeji domin ceto mutanen, bayan bincike cikin jejin yan sanda suka ceto su.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe shugabannin yan ta'adda bayan fafatawa

Shugaban matasan Kwara ya yabawa 'yan sanda

Shugaban matasan Kwara ta kudu, Olaitan Oyin-Zubair ya mika godiya ga jami'an yan sanda bisa kokarin ceto matan.

Mista Olaitan Oyin-Zubair ya ce lallai abin da jami'an tsaron suka nuna na gaggawar kubutar da matan abin a yaba musu ne.

NSCDC ta kama barayin mai

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar tsaron farar hula, NSCDC a Kano ta bayyana dakume wasu da ke kokarin safarar tankar mai zuwa jihar Katsina.

NSCDC ta kama tankar man ne a titin Ibrahim Taiwo an makare ta da lita 20, 0duk da cewa a lokacin yana matukar tsada da karanci a sassan Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng