An Fara Samun Tashin Farashin Fetur, 'Yan Kasuwa Sun Shaida Dalilin Tsadar Mai
- Rahotanni na nuna cewa an fara samun tashin farashin man fetur a wasu gidajen mai da ke yankunan jihar Lagos
- Wani dan kasuwa ya bayyana cewa su ma suna sayan mai a hannun 'yan kasuwa ne saboda haka suka daga farashin
- Shugaban kungiyar IPMAN, Alhaji Abubakar Migandi Garima ya yi karin haske kan abin da ya jawo tashin farashin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Rahotanni sun nuna cewa an fara samun tashin farashin man fetur a gidajen mai da ke cikin jihar Lagos.
Litar man fetur ta kara tsada
Binciken da jaridar Vanguard ta yi ya bayyana cewa farashin man fetur ya tashi zuwa N710 a wasu gidajen mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau tashin farashin har ya fara haddasa dogayen layuka a gidajen da suke sayar da man fetur a farashi mai sauki.
Me ya kawo tashin farashin fetur?
Wani mai sayar da mai ya bayyana cewa manyan yan kasuwa da suke sayan mai daga NNPC ne ke kara musu kudi.
Ya ce manyan yan kasuwa suna sayan lita daga NNPC a kan N548 zuwa N550 amma kuma suna sayar musu a kan N701 zuwa N705.
Farashin man fetur yanzu a Lagos
Duka da cewa gidajen man gwamnati na sayar da mai a kan N610 zuwa 568, farashin ya banbanta a wajen yan kasuwa.
Gidan man Bovas na sayarwa kan N762 duk lita, MRS na sayar da lita N735 sannan Rainoil na sayarwa kan N701 duk lita.
Shugaban kungiyar IPMAN ya yi bayani
Shugaban kungiyar masu sayar da man fetur ta IPMAN, Alhaji Abubakar Migandi ya bayyana dalilin samun tashin farashin.
Alhaji Migandi ya ce duk da kokarin da kamfanin NNPC ya ke wajen samar da mai ya gaza wadatar da dukkan masu harkar.
Saboda haka ne wasu yan kasuwar ke sayan mai da tsada ta hannun manyan yan kasuwa su kuma sai su kara riba kadan.
FRSC ta yi gargadi kan daukar fetur
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi masu abubuwan hawa kan daukar fetur a cikin jarkoki idan suna tafiya domin gujewa asarar rayuka.
Ana zargin wasu masu motoci, musamman na haya da dura fetur a jarka suna guzurinsa gudun man ya kare a hanya kuma babu mai a kusa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng