"Akwai Matsala": ASUU Ta Sanar da Shirin Shiga Yajin Aiki a Dukkan Jami'o'in Najeriya

"Akwai Matsala": ASUU Ta Sanar da Shirin Shiga Yajin Aiki a Dukkan Jami'o'in Najeriya

  • Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta jima tana faɗi-tashin a kara yawan kasafin ilimi da kuma inganta walwalar mambobinta
  • A ranar Talata, 21 ga watan Mayu, 2024 ASUU ta bayyana cewa za ta ayyana shiga yajin aiki kowane lokaci daga yanzu
  • Yayin da wa'adin mako biyu yake ƙarewa ranar Lahadi mai zuwa, ASUU ta buƙaci Gwamnatin Tinubu ta yi ƙoƙarin hana shiga yajin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta ce da yiwuwar za ta ayyana shiga yajin aiki kowane lokaci daga yanzu.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ƙeƙashe ƙasa, ta ƙi cika wa ASUU bukatunta duk da hakuri da tunin da ƙungiyar ta jima tana yi.

Kara karanta wannan

"Zamu karɓe wasu jihohi," Ganduje ya bayyana abubuwa 2 da APC ta shirya a 2027

Tinubu da shugaban ASUU.
ASUU ta ce za ta shiga yajin aiki a faɗin Najeriya kowane lokaci daga yanzu Hoto: @OfficialABAT, @ridoradeola
Asali: Twitter

ASUU ta shirya shiga yajin aiki

Farfesa Adelaja Odukoya, shugaban ASUU na shiyyar jihar Legas ya tabbatar da cewa yajin aikin malaman jami'o'i na nan tafe idan gwamnati ba tayi abin da ya dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Odukoya ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a jami'ar Legas (UNILAG) ranar Talata, 21 ga watan Mayu.

Ya ce a halin yanzun dai hakurin ASUU ya fara ƙarewa kan halin ko in kula da gwamnatin tarayya ke nunawa bukatun kungiyar, Tribune Nigeria ta tattaro.

'Yan ASUU ba su tsoron rasa albashi?

Farfesa Udokoya ya ce a mafi akasarin batutuwan da malaman ke bukatar a magance, babu ɗaya da gwamnati ta yi tsawon shekarun nan.

Malamin ya kuma yi watsi da barazanar aiwatar da tsarin 'ba aiki ba biyan albashi' inda ya ƙara da cewa babu tsarin a dokar ma'aikata ta duniya.

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

Bugu da ƙari, jagoran na ASUU ya ce ba gudu ba ja da baya, kungiyar ba za ta hakura ta daina fafutuka domin inganta harkokin ilimin jami'o'i a ƙasar nan ba.

NLC ta sake ja da gwamnati

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta sake fuskantar tirjiya daga ƴan kwadago bayan gabatar da sabon mafi ƙarancin albashi a karo na biyu.

Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya sun sake yin watsi da tayin N54,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a taron yau Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262