Bola Tinubu Ya Nuna Damuwa da Harin Masallaci a Kano, Ya Aike da Saƙo Gaa Gwamna Abba
- Mai Girma Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya da jaje ga gwamnatin jihar Kano sakamakon harin da aka kai masallaci
- Shugaban ƙasar ya umarci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan abin da ya faru, wanda ya zama ajalin masallata sama da 15 a Kano
- Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu kana ya roƙi Allah ya bai wa waɗanda ke kwance suna jinya lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Bayan kusan mako ɗaya, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa sakon ta'aziyya ga gwamnatin jihar Kano kan harin da aka kai masallaci a jihar.
Shugaba Tinubu ya yi jimamin harin wanda ya zama ajalin mutane aƙalla 17 a Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.
Saƙon Bola Tinubu na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Talata, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi tir da harin wanda wani matashi ɗan kimanin shekaru 38, Shafi'u Abubakar ya bankwa mutane wuta suna cikin sallar asubah a masallaci ranar Laraba da ta wuce.
Bola Tinubu ya ɗauki mataki
Shugaban ƙasar ya umarci hukumomin tsaro sun tabbatar sun gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban ƙuliya, Tribune Nigeria ta rahoto.
Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan mamatan, da duk wadanda abin ya shafa, ya kuma yi addu’ar samun sauki ga wadanda ke kwance suna jinya a asibiti.
Idan baku manta ba ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, Shafi'u ya farmaki masallaci a Larabar Abasawa, inda aka ce ya watsa fetur tare da kulle ƙofofi daga bisani ya cinna wuta.
Rahotanni sun nuna zuwa yanzu mutum 17 suka kwanta dama sakamakon lamarin yayin da wasu da dama suka jikkata.
Shafi'u ya gaya wa ƴan sanda cewa ya aikata wannan ɗanyen aiki ne domin koyawa wasu ƴan uwansa darasi, waɗanda yake ganin sun zalunce shi a rabon gadon gidansu.
Abba ya ziyarci masallatan da aka ƙona
A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ziyarci masallatan da aka kona a wani masallaci da ke karamar hukumar Gezawa.
Gwamnan ya ce zai rattaba hannu kan hukuncin kisa idan shi ne kotu za ta yanke wa wanda ya aikata laifin ba tare da jinkiri ba.
Asali: Legit.ng