Naira Ta Sake Rikita Dala Bayan Darajarta Ta Karu da 1.89% a Kasuwa

Naira Ta Sake Rikita Dala Bayan Darajarta Ta Karu da 1.89% a Kasuwa

  • Yayin da ake ci gaba da hada-hadar kudi a Najeriya, Naira ta sake samun galaba kan dala a kasuwar gwamnati
  • Darajar Naira ta sake yin sama inda ta karu da kusan N28 a jiya Litinin 20 ga watan Mayu a kasuwanni
  • Wannan ya biyo bayan shan bugu da Naira ta yi a hannun dala tsawon makwanni biyu kafin farfadowarta yanzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Darajar Naira ta sake tashi a kasuwar gwamnatin inda ta karu da N28 a jiya Litinin 20 ga watan Mayu.

Wannan tashi na darajar Naira ya nuna ta karu da 1.89% idan aka kwatanta da ranar Juma'a 17 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Naira ta sake tashi a karo na 2 a cikin mako 1, ta karu da kusan N100

Naira ta sake tashi a kasuwa kan dala da N28
Darajar Naira ta sake tashi inda ta kuma kassara dala a kasuwa. Hoto: Centre Bank of Nigeria.
Asali: UGC

Yanayin hada-hadar Naira da dala a kasuwa

A ranar Juma'a 17 ga watan Mayu an siyar da dala kan N1,497 idan aka kwatanta da jiya Litinin 20 daga watan Mayu da aka siyar kan N1,468, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan hada-hadar dala a kasuwa ya karu daga $83m a ranar Juma'a zuwa $161m a jiya Litinin 20 ga watan Mayu, cewar rahoton Vanguard.

Naira tana samun galaba kan dala

Wannan na zuwa ne yayin da Naira ke ci gaba da samun galaba kan dala a ƴan kwanakin nan bayan faduwarta tsawon mako biyu.

Hakan bai rasa nasaba da tsare-tsaren da Babban Bankin CBN yake ci gaba da kawowa a harkar hada-hadar kudi.

Sai dai duk da haka wasu na ganin matakan bankin CBN kara rikita Naira ya ke yi madadin ya daidaita ta.

Kara karanta wannan

Naira ta sake samun galaba kan dala bayan ƙaruwa da 4.04% a kasuwa

An bukaci Tinubu ya kori gwamnan CBN

A wani labarin, kun ji cewa an buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso da ministan kudi, Wale Edun.

Rilwan Olanrewaju, jigo a babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ya yi wannan kira yayin hira ta musamman da jaridar Legit.ng.

Ya ce babu dalilin ɗaukar mataki kan manhajar hada-hadar kudin intanet watau Binance idan har gwamnan CBN da Mista Edun sun yi aikin da ya dace game da tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel